Lauyoyi daban-daban sun bayyana cewa nadin da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi wa sabbin Shugabannin Tsaro na sojojin Najeriya haramtacce ne, domin ya karya Dokokin Najeriya kuma ya yi fatali da abin da Kundin Dokokin Sojojin Najeriya.
A ranar Talata ce dai aka nada sabbin shugabannin tsaron Najeriya kuma su ka gana da Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Alhamis, su ka kama aiki a ranar Alhamis din.
Shugaba Muhammadu Buhari ya gargadi sabbin Shugabannin Tsaron Kasa da su kasance masu kishin kasar su tare da yi wa kasar su aiki bakin-rai-bakin-fama.
Ya yi wannan kira da kuma gargadi a gare su a ganawar farko da ya yi a su a Fadar Shugaban Kasa, a ranar Laraba, wadda ita ce ganawar farko tun bayan nada su da ya yi a ranar Talata.
Ministan Tsaro Bashir Magashi ne ya jagorance su a wajen taron, wanda shi ma tsohon soja ne da ya yi ritaya ya na Manjo Janar.
Cikin wata sanarwa da Kakakin Yada Labarai na Shugaba Buhari ya fitar bayan ganawar ta su, Femi Adesina ya ce Buhari ya gargade su cewa sai fa sun tashi tsare, domin Najeriya na cikin halin ta-baci, wato an shiga ‘la haula wa la kuwwata’ a matsalar tsaro.
“Mu na cikin halin ‘la haula wa la kuwwata. Sai kun jajirce sosai kun yi wa kasar nan aiki tukuru. Saboda ku fa dama biyayyar ku ba wani ku ke wa ba, sai kasar nan kawai.”
“Babu wani abu da zan iya fada maku dangane da aikin soja wanda ba ku sani ba. Domin har yanzu a cikin sa ku ke. Sannan ina tabbatar maku duk wani abu da zan iya yi a matsayi na na Babban Kwamandan Askarawan Najeriya, to zan yi maku domin ku kai ga nasarar da jama’a za su yi murna da ku.
“Kun san dai halin da mu ka tsinci kan mu a 2015 lokacin da mu ka karbi mulki. Kun kuma san halin da mu ke a yanzu. Kuma ku na sane da alkawarin da mu ka yi wa jama’a. Mun yi masu alkawarin samar da tsaro a kasar nan. Duk abin bai zo mana da sauki ba. Amma dai mun samu ci gaba bakin gwargwado.”
Lauyoyin da su ka yarda su ka yi magana da PREMIUM TIMES sun bayyana cewa kwata-kwata nadin sabbin shugabannin tsaron ya kauce wa Dokar Najeriya da gaba dayan kundin dokar na 1999. Har ma da Dokar Sojji ta Najeriya.
Babban Lauya dan rajin kare hakkin jama’a, Femi Falana ya bayyana cewa ya na mamakin irin wannan gurunduma da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi, inda ya nada sabbin shugabannin tsaro, ba tare da amincewar Majalliasar Tarayya ba.
“Don haka wannan a maganar gaskiya kamar yadda doka ta tanadar, ba nadi ba ne, bayyana sunayen su kawai ya yi. Ba za su zama halastattun shugabannin tsaro ba, har sai ranar da Majalisar Tarayya ta amince da su tukunna.”
Falana ya ce kamata ya yi a ce an bi doka, a Buhari ya mika sunayen su ga Majalisar Dattawa, su kuma su gayyace su omin su tantance su daya bayan daya.
Falana (SAN) ya ce a ka’idance kuma a dokance, har yanzu nadin su bai tabbata ba tukunna, har sai Buhari ya mika sunayen su ga Majalisar Dattawa an tantance su tukunna. Kamar dai yadda kundin tsarin mulkin Najariya da kuma Kundin Dokokin Aikin Sojan Najeriya su ka shimfida.
“Wannan abu karara haka ya ke, Buhari ya tabka barababiya da shirme. Ba su tabbata ba har sai Majalisar Dattawa ta Tantance su tukunna. Kuma Buharin ne da kan sa zai aika da sunayen su ga Majalisa, sannan a gayyace su domin a tantance su.
“Irin haka ta faru inda cikin Festus Keyamo, wanda a yanzu Minista ne a karkashin mulkin Buhari, ya kai kasar Shugaban Kasa cikin 2008, a shari’a mai lamba FHC/ABJ/CS/611/2008.”
“A hukuncin da Mai Shari’a Adamu Bello ya ce haramun ne Shugaban Kasa ya nada Shugabannin Tsaron Kasa haka kawai kai-tsaye, ba tare da ya fara tura sunayen su Majalisa ta tantance ba. Saboda haka doka ta Sashe na 18 (1) & (3) na Dokar Sojan Najeriya ta shimfida.”
Sannan kuma Falana ya ce wancan hukunci da aka yanke ya zauna, ya kara tabbata doka, domin Gwamnatin Tarayya ba ta daukaka kara ba.
Shi ma wani lauya Jiti Ogunye, tun a cikin wani ra’ayi da PREMIUM TIMES ta buga cikin 2014, ya bayyana cewa Shugaban Kasa radin kan sa shi kadai ba shi da iznin nada shugabannin tsaro, har sai ya fara aikawa da sunayen su Majalisar Dattawa ta tantance tukunna.
Ya yi rubutun ne ganin yadda a cikin 2014 tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya nada Alex Bade Babban Hafsan Tsaron Kasa.
Sai dai ba a sani ba ko Shugaba Buhari ya aika da sunayen a Majalisa. Idan ma ya aika, to ba a dai tantance su din ba.
Kakakin Yada Labarai na Shugaban Majalisar Dattawa, Ola Awoniyi, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa ba shi da masaniyar ko an aika da sunayen.
An tuntubi Keyamo dangane da karar da ya taba kaiwa kan nada Hafsoshin Tsaron Kasa ba bisa ka’ida kuma ya yi nasara.
Keyamo wanda a yanzu Minista ne a Gwanatin Buhari, ya ce ya na nan kan goyon bayan wancan hukunci da kotu ta yanke a lokacin.
A lokacin dai, baya ga haramta nadin da aka yi, kotun ta kuma haramta wa kowane shugaban kasa na Najeriya sake nada shugabannin tsaro ba tare da fara mika sunayen su majalisa ta tantance ba tukunna.
Buhari ya aika wa Majalisar Dattawa neman amincewa da sabbin Shugabannin Tsaro
Shugaba Muhammadu Buhari ya aika wa Majalisar Dattawa wasikar neman amincewar su da sunayen manyan hafsoshin sojoji hudu da ya nada matsayin Shugabannin Tsaron Kasa.
Ya nada su a ranar Talata, jim kadan bayan sauke su Janar Buratai a ranar.
PREMIUM TIMES ta buga labarin cewa Buhari ya tsige Buratai da sauran Manyan Hafsoshin Tsaro, ya nada sabbi
Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da takardar sanarwar ajiye aiki da Manyan Hafsoshin Tsaron Kasa su hudu su ka yi.
Wadanda su ka ajiye aikin sun hada da Hafsan Hafsoshin Sojoji, Tukur Buratai, Babban Hafsan Tsaron Kasa, Janar Abayomi Olonisakin, Babban Hafsan Sojojin Ruwa, Vice Admiral Ibok Ibas da kuma Air Marshal Sadique Abubakar, Babban Hafsan Sojojin Sama.
Wata sanarwa da Kakakin Yada Labarai na Shugaba Buhari, Femi Adesina ya wallafa a shafin sa na Facebook, ta ce Buhari ya yi wa hafsoshin fatan alheri a dukkan al’amurran da su ka sa gaba bayan ritayar da su ka yi.
An maye guradun su da Manjo Janar Leo Irabor, matsayin Babban Hafsan Tsaron Kasa, Manjo Janar I Attahiru, matsayin Babban Hafsan Sojoji wanda ya canji Buratai, Rear Admiral A.Z Gambo, Babban Hafsan sojojin Ruwa, sai kuma Air-Vice Marchal I.O Amao, Babban Hafsan Sojojin Sama.
Buhari ya taya sabbin manyan hafsoshin kasar da ya nada murna, kuma ya yi horo gare su su kasance masu biyayya da aiki tukuru kan ayyukan da aka dora wa kowanen su.
Cikin wata sanarwa da Mashawarcin Musamman A Fannin Majalisar Dattawa, Babajide Omoworare, ya ce Buhari ya aika da wasikar ga Shugaban Majalisar Dattawa tun a ranar 27 Ga Janairu.
Ya ce an yi haka kamar yadda Sashe na 18 (1) na Dokar Aikin Soja ta Najeriya ta tanadar.
Ya ce ba gaskiya ba ne da ake cewa an nada su ba tare da an sanar da Majalisar Dattawa ba.
Discussion about this post