Tsohon Babban Hafsan Sojojin Najeriya, Tukur Buratai, ya bayyana cewa ya sauka daga aikin shugabancin Rundunar Sojojin Najeriya bayan ya yi aiki tukuru, wanda ya fi yadda ya samu hukumar tsaron sojojin.
Buratai ya yi wannan uruci a lokacin da ya ke jawabin bankwana a yayin wani faretin bankwanan da aka shirya masa, ranar Laraba, a Hedikwatar Askarawan Najeriya, Abuja.
Ya ce a karkashin shugabancin sa sojoji sun samu nasarar yaki da masu ta’addanci da kuma sauran masu kawo wa tsaron kasar nan barazana.
Ya ci gaba da cewa a zamanin sa ya tabbatar da sojoji sun samu ingantaccen horo tare da karin kulawa da jin dadin su.
“Yau rana ce ta farin ciki da nuna matukar godiya, amma bari na shaida wa kowa cewa na tafi na bar Rundunar Askarawan Najeriya fiye da yadda na same ta a farkon hawa na.
“Sojojin Najeriya a karkashi na sun samu gagarimar galaba kan Boko Haram a fadin kasar nan.
“Mun rika samun barazana nan da can, amma dai ina tabbatar maku da cewa babu wani sashe ko bangare ko yanki na Najeriya da a yanzu ya ke a hannun ‘yan ta’adda. Ko wasu masu kai hare-hare.
“Yakin sunkuru a baya ya kasance bakon abu ga sojojin Najeriya, amma ahankali mun samu hanyoyin dakile wannan babbar barazana a cikin kasar nan.
Buratai ya yi kira ga sojojin Najeriya su ci gaba da nuna kwazo, juriya da kuma kishi wajen yaki da ta’addanci da kuma sauran matsalolin tsaron da su ka addabi kasar nan.
Buratai ya gode wa ojojin Najeriya kan hadin kai da aka ba shi, kuma ya gode wa gwamantin jihar Barno da sauran wadanda su ka goya bayan sojoji sun yi nasara a zamanin sa.
A karshe ya roki ‘yan siyasa da su kauda kai daga kokarin tsoma sojoji a cikin siyasa.
Discussion about this post