Na daina magana kan gwamnatin Buhari, kada hawan jini ya kama ni – Soyinka

0

Wole Soyinka ya bayyana cewa ya daina magana kan matsalolin gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari, saboda gudun kada rashin lafiyar hawan jini ta kama shi.

Ya ce duk mai so ya gama lafiya, to ya kudurta a ran sa cewa babu wata gwamantin mai suna gwamnatin Buhari da ke mulkin Najeriya.

“Mantawa da Buhari na mulki zai rage wa mutum haushi da takaici. Domin gudun kada ciwon hawan jini ya kama mutum, to mafiya kawai ya daina tunawa da wata gwamnatin da ake kira gwamnatin Buhari.” Inji Soyinka.

Ya yi wannan bayani ne ga wani wakilin gidan talbijin na Kaftan TV, yayin da ya ke cikin jirgin kasa daga Lagos zuwa Ibadan.

“Ba zan so yin magana kan wai ko jirgin kasa wata gagarimar nasara ce a gwamnatin Buhari ba.”

Sai dai kuma ya ce samar da jirgin kasa din zai bunkasa kasuwanci.

Ya tuna yadda ya fara hawa jirgin kasa lokacin ya na karamin yaro daga Abeakuta zuwa Lagos zuwa Ibadan.

Sai ya kara da cewa a yanzu kuwa cinkoson motoci ya yi yawa matukar gaske.

“Tsakanin Lagos zuwa Abeakuta na shafe awa bakwai cikin makon da ya gabata, a okacin da na tafi kaddamar da littafi na.”

Batun jirgin kasa kuwa, a iya cewa an fara wani abu, idan aka yi la’akari da ganin cewa babu wani abin kirkin da za yi bugun kirji da shi.”

Duk da haka ya ce amma a yau zai iya hawa jirgi daga Abeakuta ya je Lagos ko Ibadan ya koma gida duk a rana daya.

PREMIUM TIMES HAUSA ta buga wata hira da shi ta ranar 10 Ga Disamba, 2020, inda ya bayyana cewa “ai yi wuya mai hankali ya yarda cewa akwai mai rike da akalar Najeriya a yanzu”

Fitaccen mai fada a ji Wole Soyinya, ya bayyana cewa zai yi wahala a tunkari mai hankali a ce masa akwai mai rike da akalar Najeriya a halin yanzu, kuma har ya yarda.

Soyinka ya ce a gaskiya Najeriya ba ta da shugabanni masu hangen nesa kwata-kwata.

Ya yi wannan bayani ranar Laraba, lokacin da ya ke magana kan kalubalen da Najeriya ta fuskanta cikin 2020.

Ya ce shekarar 2020 ita ce shekarar da ya yanke kauna kan lamuran gyaran kasar nan, saboda babu shugabanni masu hangen nesan da za su iya tsamo ta daga dagwalon da su ka jefa ta, har su yi mata wankan sake tsaftace ta.

Ya yi bayanin a Ibadan, wurin kaddamar da littafin sa mai suna, “The chronicles of the happiest people on earth”, wato ” Jadawalin mutanen da su ka fi rayuwar farin ciki a duniya. ”

Soyinka ya ce ya shafe shekaru 40 cur ya na tattara bayanan da ke cikin littafin mai shafuka sama da 500.

“Irin yadda shekarar 2020 ta zo sabubba marasa dadi da dama, kuma ga shi har shekarar ta zo karshe, amma har yanzu mun kasa hudu, sai tuma tsalle kawai mu ke yi wuri daya.

“Ba na so a ga kamar ina ta kiran jafa’i, amma dai ni wannan shekara ce na fi yanke kauna kan Najeriya. Ba wai don saboda barkewar korona ba. Masifu da bala’o’i sun faru, kuma har yanzu ha shekarar ta zo karshe, amma agiya na jike, an kasa daure kaya.”

“Shin masifun nan sun faru ne saboda kaddara ko kuwa dalilin sakacin wadanda ke ganin kamar alfarma su ke wa matane don su na shugabantar su?

“Gaskiyar magana ba haka ya kamata kasa ta ci gaba da wanzuwa ba. Na haka ya kamata dan Adam ya ci gaba da rayuwa ba. Yanzu abin ya kai makurar da idan ka fita, ba ka ma san inda za ka ba. Kuma ba ka ma san iyar inda za ka yada zango ba.”

“Kamar yadda na sha fada a baya, yanzu ma ina kara fadi, an kai munzilin da wahala mutum ya yarda cewa akwai masu jan akalar Najeriya a yanzu.”

Share.

game da Author