Sifeton-janar din ‘Yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu, ya umarci kwamishinar ‘ƴan sandan jihar Oyo, Ngozi Onadeko, ta taso masa keyar wani wai mai fafutikar kare hakkin ‘yan kabilar Yarabawa mai suna Sunday Adeyemo da aka fi sani da Igboho cikin gaggawa a kawo masa shi Abuja.
BBC HAUSA ta ruwaito cewa kakakin fadar gwamnatin Buhari Garba Shehu ya bayyana mata cewa da kansa ya nemi tabbacin hakan daga bakin Sifeton ‘yan sandan Adamu kasa kuma ya tabbatar masa da haka.
BBC Hausa ta ce Garba Shehu ya shaida mata a hira da ta yi da shi a shirinta na Ra’ayi Riga, cewa ko a lokacin da suke hirar bai dade ba da ya tattauna da sifeto Adamu din game da wannan kamu da yasa ayi wa Igboho.
Shehu ya kara da cewa gwamnati na fuskantar matsaloli wajen hukunta masu laifuka saboda yadda kungiyoyin da ke ikirarin masu kare hakkin dan Adam ne ke yi musa katsalandan a ayyukan su na da sunan wai kare hakkin mutane.
Har yanzu ana ta cacanbaki tsakanin wasu gwamnonin yankin Kudu Maso Yamma da musamman kungiyoyin fulani makiyaya tun bayan shata musu iyaka da gwamnan Ondo Rotimi Akeredolu yayi wa fulani a jihar da kuma fatattakar su daga yin kiwo a dazukan jihar Ondo.
Ko da yake gwamnan jihar Oyo Seyi Makinde ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda ake muzguna wa makiyaya inda umarci wadanda ke zaune a jihar su ci gaba da zama a yanki.
Hakan ya jawo cece-kuce a tsakanin sa da wasu yan kabilar Yarabawan a yankin.
Discussion about this post