Ministan ilimi Adamu Adamu ya ce an samu raguwa a yawan yaran da basu zuwa makaranta a Najeriya daga miliyan 10.1 a shekarar 2019 zuwa miliyan 6.95 a shekarar 2020.
Adamu ya fadi haka ne a taron ministocin da aka yi a Abuja ranar Alhamis.
Ya ce an samu wannan raguwa ne saboda shirin inganta ilimi da gwamnati ta shigo da shi mai taken ‘Better Education Service Delivery for All (BESDA) initiative’.
“An fara kafa wannan shiri a jihohi bakwai a kasar nan inda a dalilin nasarorin da aka samu aka kara jihohi 10 da suka hada da Adamawa, Bauchi, Borno, Ebonyi, Kano, Oyo, Yobe, Niger da Zamfara.
Adamu ya ce a yanzu haka Shirin BESDA na aiki a jihohi 17 a kasar nan. Hakan ya taimaka wajen saka yara 1,053,422 a makarantu a kasar nan.
Bayan haka ministan ilimi ya ce gwamnati ta hada hannu da kungiyar masu makarantun dake zaman kansu a kasar nan domin ganin an saka duk yaran dake gararramba a titi a makaranta.
Ya ce zuwa yanzu kungiyar ta taimaka wajen saka yara sama da miliyan daya a makaranta sannan kowace makarantar dake zaman kanta na kungiyar ta dauki nauyin biyan kudin makarantar dalibai 5.
Adamu ya ce domin karfafa wannan shiri gwamnatin tarayya ta ciyo bashin dala miliyan 611 daga babban bankin duniya domin inganta ilimi a jihohi 17.
Adamu ya kara da cewa gwamnati ta tsara wasu matakai da za su taimaka wajen saka manyan ‘yan mata a makarantu domin su samu ilimin boko tare da horas da su sana’o’in hannu. Sannan kuma bankin ya tallafa wa Najeriya da dala miliyan 500 domin wannan aiki.
Daga nan Adamu ya ce tsakanin shekarar 2019 zuwa 2020 mutum miliyan 1,900,000 ne suka koyi iya karatu, rubutu da rangaɗa turanci a ƙasar nan ta hanyar samar da Iimin yaki jahilci.
Discussion about this post