Munanan Halayen Dan Arewa 13, Daga Imam Murtadha Gusau

0

Dan Arewa Kai Kake Jawo Wa Kan Ka Bala’i!

Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jinkai

Assalamu Alaikum

Don Allah ‘yan uwa na bari in tambaye ku, shin wai me za’ayi da munanan halayen irin na Dan Arewa? Kun san dalilin wannan tambayar kuwa? To idan baku sani ba ku biyo ni sannu a hankali domin kuji. ‘Yan arewa sun dade suna cin dunduniyar junan su! Sun dade suna rusa kan su! Sun dade suna cin amanar kawunan su! Sun dade suna hasadar junan su!

Magabatan mu na kwarai, irin su marigayi Sa’adu Zungur, Allah ya jikan sa da rahama, da ire-iren sa, sun dade suna fada muna cewa, mu ‘yan arewa da zaran mun samu kawunan mu cikin irin wadannan munanan dabi’u da halaye marasa kyau, to wulakanci da kaskanci da rashin girma zasu rufe mu! Allah ya sawwake, amin.

Na farko: Shin ba Dan arewa ne ya cire Khalifah Muhammadu Sunusi I ba akan mulki, saboda yaki yi masa biyayya akan zalunci?

Na biyu: Shin ba Dan arewa ne yaci mutuncin tsohon Sarkin Kano, marigayi Ado Bayaro ba?

Na uku: Shin Dan arewa bai ci mutuncin masarautar Sakkwato ba mai daraja? Shin Dan arewa bai ci mutuncin Mai Alfarma Sarkin Musulmi ba? Wani Dan arewar ma da ya samu yadda yake so, wallahi yadda aka ci mutuncin masarautar Kano, haka shima ya sha alwashin sai yaci mutuncin masarautar Sakkwato, to amma sai Allah bai bashi nasara ba!

Na hudu: Shin Dan arewa bai ci mutuncin Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II ba, sannan ya sauke shi daga sarauta, ba don komai ba, sai domin kawai yaki yi masa biyayya akan zalunci da sharri?

Na biyar: Shin Dan arewa bai ci mutuncin Sheikh Dahiru Usman Bauchi ba, ya tura karfe sha biyun dare, aka tattara almajiransa, aka tafi dasu, daga gidansa na Kaduna ba?

Na shida: Shin ba Dan arewa bane yake fatan mutuwa da sharri ga Shugabansa, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ba?

Na bakwai: Shin ba Dan arewa bane yake tsinewa manyansa, yake zaginsu da la’antarsu ba?

Na takwas: Shin ba Dan arewa bane kadai baya girmama manyansa da na gaba da shi ba, yake daukar su ba bakin komai ba?

Na tara: Shin ba Dan arewa bane yake fatan tsiya da bala’i da fitina da tashin hankali da sharri su fadawa yankin sa na arewa ba?

Na goma: Shin ba Dan arewa bane yake girmama aljihunsa sama da yankinsa na arewa ba?

Na sha daya: Shin don Allah ba Dan arewa bane ake hada kai da shi a cutar da yankinsa na arewar ba?

Na sha biyu: Shin don Allah ba Dan arewa bane baya son cigaban dan uwansa ba, kuma yake son sharri ya auka masa ba?

Na sha uku: Don Allah ba Dan arewa bane baya son cigaban yankin sa ba?

‘Yan arewa kenan, munafunci yayi muna yawa. Muna nuna cewa mu na Allah ne, amma wallahi ta-ciki-na-ciki!

Kuma wallahi idan bamu ji tsoron Allah muka canza ba, to wulakanci da cin mutunci da bala’i da rashin tsaro, kadan kenan muka fara gani! Idan mun canza sai shima Allah ya canza muna! Allah ya sawwake, amin.

‘Yan uwa na ‘yan arewa, wallahi lokaci yayi da zamu farka daga dogon baccin da muke yi. Ba maganar kabilanci, ko banbancin yare, ko na addini a wurin ciyar da kasar mu gaba! Kuma maganar arewa da nike ta yi, ba wai ina nufin ‘yan kudu makiyan mu bane, a’a. ‘Yan uwan mu ne, mu ‘yan kasa daya ne, amma da yake kowa yana gwagwarmaya ne akan yankin sa, sai muma muyi kokarin ciyar da namu yankin gaba!

Kuma sannan ina mai jawo hankalin mu game da wani audio, na wata shedaniyar mata, tsinanniya, da ake yadawa, domin a kara rusa arewa, a jefa yankin cikin mummunan rikici tsakanin hausawa da fulani. Wannan matar da ke cikin wannan audio, muyi hankali, wallahi ba ‘yar arewa bace, kuma wallahi ba bahaushiya bace. Wata shedaniya ce kawai, aka dauki hayar ta, aka biya ta, ana amfani da ita, domin su cimma burin su na rusa muna arewa!

Tana nuna cewa wai babu ruwan mu da abun da ake yiwa Fulani a kudu. Kuma tana nuna cewa wai Fulani da hausawa makiyan juna ne. Wannan wallahi duk karya ne, kuma sharri ne da shedanci!

Hausawa da Fulani da dukkanin kabilun arewacin Najeriya ‘yan uwan juna ne wallahi. Don haka ya zama tilas mu fadaka, kar mu sake yarda a hada mu fitina da tsahin hankali da junan mu.

Wannan abu na jarabawa da yake faruwa na halin rashin tsaro, a arewacin Najeriya, don Allah muyi ta kokari da bin dukkanin hanyoyin da suka dace wurin kawo karshen shi, tare da hadawa da rokon Allah da addu’o’i. In Shaa Allahu idan munyi haka, Allah mai jin kai ne, mai tausayin bayin sa ne, zai tausaya muna, ya dauke muna wannan jarabawa.

Amma don Allah kar mu saurari duk wasu masu kokarin kara rura wutar rikici a duk inda suke, kuma ko su wanene!

Allah yasa mu dace, amin.

Dan uwan ku: Imam Murtadha Muhammad Gusau, daga Okene, Jihar Kogi, Najeriya. Za’a iya samun sa a lambar waya kamar haka: 08038289761.

Share.

game da Author