MATSALAR TSARO: Ku yi wa kasar ku aiki bakin-rai-bakin-fama – Sakon Buhari ga sabbin Shugabannin Tsaro

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya gargadi sabbin Shugabannin Tsaron Kasa da su kasance masu kishin kasar su tare da yi wa kasar su aiki bakin-rai-bakin-fama.

Ya yi wannan kira da kuma gargadi a gare su a ganawar farko da ya yi a su a Fadar Shugaban Kasa, a ranar Laraba, wadda ita ce ganawar farko tun bayan nada su da ya yi a ranar Talata.

Ministan Tsaro Bashir Magashi ne ya jagorance su a wajen taron, wanda shi ma tsohon soja ne da ya yi ritaya ya na Manjo Janar.

Cikin wata sanarwa da Kakakin Yada Labarai na Shugaba Buhari ya fitar bayan ganawar ta su, Femi Adesina ya ce Buhari ya gargade su cewa sai fa sun tashi tsare, domin Najeriya na cikin halin ta-baci, wato an shiga ‘la haula wa la kuwwata’ a matsalar tsaro.

“Mu na cikin halin ‘la haula wa la kuwwata. Sai kun jajirce sosai kun yi wa kasar nan aiki tukuru. Saboda ku fa dama biyayyar ku ba wani ku ke wa ba, sai kasar nan kawai.”

“Babu wani abu da zan iya fada maku dangane da aikin soja wanda ba ku sani ba. Domin har yanzu a cikin sa ku ke. Sannan ina tabbatar maku duk wani abu da zan iya yi a matsayi na na Babban Kwamandan Askarawan Najeriya, to zan yi maku domin ku kai ga nasarar da jama’a za su yi murna da ku.

“Kun san dai halin da mu ka tsinci kan mu a 2015 lokacin da mu ka karbi mulki. Kun kuma san halin da mu ke a yanzu. Kuma ku na sane da alkawarin da mu ka yi wa jama’a. Mun yi masu alkawarin samar da tsaro a kasar nan. Duk abin bai zo mana da sauki ba. Amma dai mun samu ci gaba bakin gwargwado.”

Buhari ya nuna masu bukatar kara wa sojoji na kasa da su kwarin guiwa da kuma alkawarin kasa samar da makaman kakkabe duk wata matsalar tsaron da ta dabaibaye kasar nan.

Share.

game da Author