Matasa 774,000 da aka zaba domin aiki na Musamman, za su fara a ranar Laraba.
An dai dauki matasan 1,000 a kowace Karamar Hukuma ce domin yin ayyukan da za a rika biyan su naira 20,000 duk wata.
Sanarwar fara aikin na su ya fito ne a bakin Ministan Harkokin Yada Labarai, Lai Mohammed, a lokacin da ya ke ganawa da manema labarai a Lagos, a ranar Litinin.
Ya ce gwamnati ta kaddamar da shirin Karfafa Jarin Matasa da naira bilyan 75, wato NYIF, kuma matasa masu shekaru 18 zuwa 35 ne za su ci gajiyar shirin.
A jawabin sa, ya kara da cewa makasudin kirkiro shirin shi ne domin matasan Njariya su a kalla 500,000 su samu ayyuka tsakanin 2020 zuwa 2023.
Lai y ace Gwamnatin Buhari ta kirkiro shirye-shiryen tallafa wa iyalai, kanana da matsakaitan masana’antu ko harkokin kasuwanci, sakamakon kuncin rayuwar da barkewar cutar korona ta haifar a kasar nan.
Ya kara da cewa nan da watanni 12 za a wadata ’yan Najeriya akalla milyan biyar da wutar lantarki ta sola, mai amfani da hasken rana.
Sannan ya ce shirin zai samar da aikin yi ga matasa 250,000 tare da samar wa wasu mutum milyan 25 tagomashi kai-tsaye.
Ya ci gaba da nanata irin tsare-tsaren inganta rayuwar talaka da Gwamnatin Tarayya ta bijiro da su, irin su Trader Moni da Market Moni.
Sannan kuma ya ce akalla gidaje milyan 8.8 ne su ka ci gajiyar tallafin abinci na metric tan 70,000 da gwamnati ta fitar daga Manyan Rumbunan Gwamnatin Tarayya.
“Gidaje milyan 1.3 su ka ci gajiyar Kudaden Rage Radadin Talauci da ake tura masu kai-tsaye ta asusun ajiyar su na banki a fadin jihoh 34.”
Mimista Lai ya yi bayanin irin tsare-tsaren inganta harkokin kasuwanci, noma da rage radadi da Babban Bankin Najeriya, CBN ya kirkiro tun bayan barkewar cutar korona.