A ƙarƙashin Shirin Bada Tallafin Kuɗi ga Matan Karkara da Gwamnatin Tarayya ke aiwatarwa, aƙalla mata 8,000 ne za su amfana a ƙananan hukumomi 44 da ke Jihar Kano.
Ministar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa, Sadiya Umar Farouk, ita ce ta bayyana haka a wajen bikin ƙaddamar da shirin wanda aka yi a Kano a ranar Litinin.
A yayin da ta ke magana ta bakin Babban Sakataren ma’aikatar, Bashir Alƙali, wanda ya wakilce ta a bikin, ministar ta bayyana cewa an fito da shirin ne a cikin 2020 domin a faɗaɗa shirin gwamnatin Shugaba Buhari na rage wa talakawa matsalolin rayuwa.
Ta ce: “An tsara shi ne domin a samar da tallafi biya ɗaya ga matan da su ka fi kowa fatara da matsalolin rayuwa a yankunan karkara da gefen birane na ƙasar nan.
“Za a bada tallafin tsabar kuɗi N20,000 ga kowace a cikin kimanin mata faƙirai guda 125,000 a dukkan jihohi 36 na ƙasar nan da Yankin Babban Birnin Tarayya.”
Ministar ta ƙara da cewa ana sa ran tallafin zai ƙara wa waɗanda aka ba hanyoyin samun kuɗin shiga.
Hajiya Sadiya ta yi kira ga waɗanda su ka amfana da shirin da su yi amfani da kuɗin wajen bada gudunmawa ga inganta rayuwar su ta yau da kullum.
Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje, a jawabin sa, ya yaba wa gwamnatin Shugaba Muhammad Buhari saboda fito da shirye-shirye da ta yi don ɗaga rayuwar jama’a da rage masu wahalhalun rayuwa, musamman mata da ƙananan yara.
Ya jinjina wa ma’aikatar saboda damar da ta ba Jihar Kano don matan karkara na jihar.
A ƙarƙashin shirin Bada Tallafin Kuɗi ta hanyar Tiransifa kuwa, wato Conditional Cash Transfer (CCT), gwamnan ya ji daɗin yadda aka ƙara ɗibar mata guda 35,000 daga ƙananan hukumomi 15 na jihar, sannan ya yi kira ga ministar da ta amince a ɗauki ragowar mata 35,000 daga waɗannan ƙananan hukumomin.
Ganduje, wanda Mataimakin Gwamna, Yusuf Gawuna, ya wakilta a bikin, ya buƙaci a faɗaɗa Rajistar Jama’a ta jihar don a haɗa da sauran ƙananan hukumomi 29 na jihar waɗanda su ka rage, da kuma ƙarin sauran shirye-shiryen bada lamuni (irin su Trader Moni, Market Moni da Farmer Moni) a zagaye na gaba na shirin, da sauran su.
A wani labarin makamancin wannan, an bayyana cewa sama da mata 4,000 a cikin ƙananan hukumomi 27 da ke Jihar Jigawa ne za su amfana daga wannan shiri na Gwamnatin Tarayya na bada tallafin kuɗi ga matan karkara.
Minista Sadiya Farouq ce ta bayyana hakan a wajen bikin ƙaddamar da shirin wanda aka yi a Dutse, babban birnin jihar.
Ta ce, “Ina ta lura da ƙoƙarin inganta jihar wanda mai girma Gwamna ke yi, kuma na tabbatar idan an ci gaba da wannan gagarumin aiki, to, tsare-tsare da shirye-shirye daban-daban da gwamnatin Shugaba Buhari ke yi za su yi tasirin da ake buƙata a rayuwar al’ummar Jihar Jigawa.”
Ministar ta yi kira ga dukkan masu ruwa da tsaki a lamarin da su mara wa Gwamnatin Tarayya baya a ƙoƙarin da ta ke yi na magance matsalolin da su ka danganci cigaban ƙasar nan.
Gwamnan Jihar Jigawa, Muhammad Badaru wanda ya yi magana ta bakin mai ba shi shawara na musamman kan ƙarfafa tattalin arziki, Abba Mujaddadi, ya yaba wa shirin na Gwamnatin Tarayya, sannan ya yi la’akari da cewa Jihar Jigawa ta amfana da sauran shirye-shiryen magance fatara na Gwamnatin Tarayya a baya, wato irin su GEEP, CCT, HGSFP, da sauran su.
Gwamnan ya yi kira ga waɗanda su ka ci moriyar shirin da su yi amfani da kuɗin ta hanyar da ta dace domin taimakon kan su da iyalan su.