Ogundele Olubukola babban jami’in binciken kimiyya ne a Jami’ar Gona ta Gwamnatin Tarayya ta Abeokuta (FUNAAB). Ya shafe shekara 10 cur ya na kiwon zuma, inda a duk wata ya na samun ruwan zuma lita 150.
Kuma duk wannan zuwa mai tarin yawa da ya ke samu a duk wata, gidan zuma wato amiya guda 85 ce ya ke da ita.
A yanzu ana sayar da kowace lita daya naira 1,200. Yawan bukatar zuma a wannan lokaci ya nuna cewa jama’a su na ci gaba da yawan ja baya daga amfani da sukari.
Kuma kiwon zuma kenan zai rika samar da ayyukan yi ga dimbin jama’a kenan.
“Ai yanzu ne ma kasuwar bukatar zuma ke kara hauhawa sosai. Hakan kuma mu na yin la’akari ne da yawan bukatar ta da ake yi daga gare mu.
“Babban nasibin kasuwancin zuma shi ne idan jama’a su ka san cewa zumar ka gangariya ce babu hadi da sukari, to za a rika neman zuma a hannun ka afujajan.” Inji Olubukola.
Sannan kuma abin alheri ga noman zuma shine mutum zai iya yin kiwon zuma a lokaci guda kuma ya na can ya na aikin sa. Aikin sa bai samu tawaya ba, kuma kiwon zumar sa ma ba zai samu cikas ba.
Masana dabarun kula da lafiyar jiki sun bayyana cewa ruwan zuma ya na da amfani matuka, shi ya sa jama’a ke kauce wa sukari sun a tururuwa wajen rika yin amfani da zuma.
Duk da nasibi da kudin da ake samu a kiwon zuma, masu wannan sana’a da su ka yi hira da PREMIUM TIMES sun nuna cewa tabbas ana samun kudi, amma kuma a Najeriya har yanzu mutanen da su ka dauki kiwon zuma da muhimmanci, kalilan ne, ba su da yawa.
Wani mai suna Elumezie Ifeanyichukwu, ya ce shekara uku kenan ya na kio-won zuma, kuma sana’ar ba ta kawo masa tawaya ga aikin sa ba.
“Na fara da gidan zuma daya, inda na kan samu lita 15 zuwa 20, amma a yanzu ina da gidan zuma har 23” Inji shi.
Shi kuma agunduro Gideon ya fara sana’ar kiwon zuma shekaru 25 da su ka gabata da gidan zuma 20. Amma a yanzu ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa ya na da gidan zuma har 2,000.
Dagunduro ya ce a shekara ya na samun ruwan zuma har tan biyar. Shi ne ma Shugaban Kungiyar Masu Kiwon Zuma na Najeriya.
Ya nuna wa wakilin mu yadda ya ke tara ruwan zuma da kuma inda ya ke kiwon zuma a Gwagwalada.
Da yawan wadanda su ka yi hira da PREMIUM TIMES sun nuna cewa akwai bukatar Ma’aikatar Ayyukan Gona ta Kasa ta rika wayar wa mutane kai dangane da alfanun da ke tare da kiwon zuma.
Sannan kuma akwai bukatar a rika tallafa wa kananan manoma da abin inganta noman zuma domin a fadada hanyoyin samar da aikin yi a kasa.
Discussion about this post