Masu haɗa baki da ƴan bindiga ne babbar matsalar rashin tsaro – Sarkin Maru

0

An bayyana cewa masu hada baki da ’yan bindiga su na kai masu rahoton wadanda za a dauke a yi garkuwa da su a samu kudi, su ne babbar matsalar rashin tsaron da ta ki ci ta ki cinyewa a Jihar Zamfara.

Mai Martaba Sarkin Maru, Abubakar Maigari ne furta haka a ranar Asabar, a Gusau, babban birnin Jihar Zamfara.

Maigari ya shaida wa sabon Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Zamfara, Abutu Yaro cewa lallai sai yan sanda sun tashi haikan sun dakile masu kai wa mahara rahotanni da kuma sanar da su irin shirin da jami’an tsaro ke yi kan su, idan ana so a gaban ’yan bindiga a jihar.

Ya yi masa wannan matashiya ce a lokacin da kwamishinan ya kai masa ziyara.

“Mu na kira ga gwamnati da kuma jami’an tsaro su kawo karshen masu hada kai da mahara ana satar mutane kuma su na sanar da ’yan bindiga shirin a jami’an tsaro ke yi.

“Mafi yawan masu kai wa ’yan bindigar nan rahoto fa duk su na cikin yankunan mu. Kuma abin mamaki jama’a sun san su. Su na nan su na ci gaba da aikata mummunan aikin da su ke aikatawa.

“Za mu yi farin ciki idan jami’an tsaro su ka yi mana maganin su gaba daya.” Inji basaraken.

Tun da farko dai Kwamishina Yaro ya shaida wa sarkin cewa ziyarar da ya kai masa, ziyarar da ya kai na daya daga cikin rangadin neman hadin kai da wadanda su ka kamata, domin a taru a kashe mahaukacin kare kowa ya huta.

Kuma nemi hadin kai da goyon bayan sauran jama’a domin a kawar da matsalar tsaro a jihar Zamfara.

Shugaban Riko na Karamar Hukumar Maru, Salisu Dangulbi, wanda shi ma ya halarci wurin, ya yi kira da a kara tura karin jami’an ’yan saanda a wasu sassa na karamar hukumar Maru, musamman a yankin Mayanci.

Share.

game da Author