Mai martaba sarkin Zazzau, HRH, Ahmed Bamalli ya nada Yeeiman Zazzau, Madakin Zazzau.
Sarautar Madaki a kasar zazzau ya dade babu wani a kai.
Wannan nade-nade na daga cikin sabbin nade-naden da Sarki Bamalli yayi a cikin makin jiya a kasar zazzau.
Yerima Mannir ya na daga cikin jerin ‘ya’yan Sarkin da suka yi mubaya’a ga sabon sarki a lokacin da gwamna Nasir El-Rufai ya nada Ambasada Ahmad Bamalli Sabon Sarki.
Sarkin Zazzau Maimartaba Ahmed Nuhu Bamalli ya nada kanin sa Mansir Nuhu Bamalli sabon magajin garin Zazzau.
Idan ba a manta ba wannan kujera ce sarki Ahmadu yake bisa kai har zuwa lokacin da gwannan Nasir El-Rufai ya nada sarkin Zazzau.
Bayan haka sarki Bamalli ya nada Abbas Tajjuddeen sabon Iyan Zazzau.
Ga yadda nade-naden suke:
1. Mansur Nuhu Bamalli daga saraiutar Barde Kerarriyan Zazzau zuwa Magajin Garin Zazzau.
2. Abbas Tajjuddeen sabon Iyan Zazzau.
3. Shehu Tijjani Àliyu Dan Sidi Bamalli Barden Kudun Zazzau kuma Hakimin Makera/Kakuri ya zama Barden Zazzau Barden.
4. Abdulkarim Bashari Aminu, dan marigayi Iyan Zazzau ya zama sabon Talban Zazzau.
5. Buhari Ciroma Aminu ne sabon Barde Kerarriyan Zazzau.
6. Idris Ibrahim Idris wanda shine Barden Zazzauan nada shi sabon Sa’in Zazzau.
7. An nada Aminu Iya Saidu sabon Kogunan Zazzau.
8. Tsohon mataimakin Kwantorolan Kwastam Bashir Abubakar ya zama Barden Kudun Zazzau
9. Munnir Ladan kuma ya gaji sarautar wan sa Dan Iyan Zazzau, Yusuf Ladan, sabon Dan Iyan Zazzau.
Discussion about this post