Malejin rashawa da cin hanci ya kara cillawa sama a Najeriya – Binciken TI

0

Kungiyar Bin Diddigin Ayyukan Bisa Ka’ida ta ‘Transparency International’, ta fitar da jadawalin kasashen da aka fi cin hanci da rashawa a cikin shekarar 2020, tare da cewa malejin rashawa da sikelin cin hanci a Najeriya sun kara daga wa sama a cikin 2020.

Wannan maleji da sikelin awon rashawa da cin hanci na nufin cewa matsalar ta kara muni sosai a cikin ma’aikatan gwamnatin Najeriya da shugabanni a cikin 2020.

Najeriya dai ta kara nutsawa cikin kogin rashawa da ramin cin hanci, inda ta kara nausawa kasa cikin kogin cin hanci har da karin gaba uku, daga iyar zurfin da ta ke a ciki kafin 2020.

Sabon jadawalin cin maki tsakanin kasashe masu karancin satar kudade ya nuna cewa Najeriya ta samu maki 25 bisa 100 kacal a cikin 2020, wato kasa da maki 26 da kasar ta samu a kididdigar 2019.

Najeriya ita ce kasa ta 149 a jerin kasashen da ba a satar kudaden gwamnati, daga cikin kasashe 180.

Amma kuma a cikin 2019, Najeriya ce kasa ta 146.

A cikin 2018 kuma Najeriya ta zo ta 144.

CPI na dora kasashen duniya 180 a kan sikelin malejin satar kudaden gwamnati, ba wai a kan ra’ayoyin jama’a ko masana ko manyan ‘yan kasuwa ba.

Rahoton ya nuna kasashen Denmark da New Zealand ne kasashen da aka fi sauran kasashe rikon kudaden gwamnati bil-hakki da gaskiya.

Daga su kuma sai Finland, sai Singapore da Sweden da kuma Switzerland.

Kasashe irin su Sudan ta Kudu da Somalia, wadanda yaki ya durkusar, su ne na sahun farko na lalatattun kasashe.

Sai dai kuma a duk shekara gwanatin Najeriya na yi fatali da jadawalin yadda ake dora Najeriya a sahun maciya rashawa a duniya.

Mahukuntar kasar na ganin cewa gwamnatin Muhammadu Buhari ta na matukar kokari wajen dakile cin hanci da rashawa.

Har yanzu dai Najeriya ba ta ce komai ba tukunna a kan wannan sabon rahoton da TI ta fitar.

Share.

game da Author