MALEJIN CIN RASHAWA: Fadar Shugaban Kasa ta la’anci rahoton Kungiyar TI

0

Fadar Shugaban Kasa ta la’anci rahoton Kungiyar TI, wanda ya nuna cewa Najeriya ta kara komawa sahun baya na jerin kasashen da ake ririta kudaden gwamnati da kuma rashin cin hanci da rashawa.

Rotohon dai ya nuna Najeriya na a sahun gaba na kasashen da aka fi karbar rashawa da cin hanci, sakamakon kara shiga sahun gaban da kasar ta yi a kididdigar bayanan shekarar 2020.

Kakakin Yada Labarai na Fadar Shugaban Kasa, Garba Shehu, ya bayyana cewa Gwamnatin Shugaba Muhannadu Buhari ta fara nazarin daga inda rahoton ya fito domin tantance wadanda su ka yi wannan aikin dora Najeriya a sahun gaban malalatan kasashe.

Rahoton dai ya nuna Najeriya it ace ta biyu wajen lalacewar cin hanci da rashawa a Afrika.

PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin cewa malejin rashawa da cin hanci ya kara cillawa sama a Najeriya. A labarin ta nuna Fadar Shugaba Buhari ba ta ce komai a kan batun.

Kungiyar Bin Diddigin Ayyukan Bisa Ka’ida ta Transparency International, ta fitar da jadawalin kasashen da aka fi cin hanci da rashawa a cikin shekarar 2020, tare da cewa malejin rashawa da sikelin cin hanci a Najeriya sun kara daga wa sama a cikin 2020.

Wannan maleji da sikelin awon rashawa da cin hanci na nufin cewa matsalar ta kara muni sosai a cikin ma’aikatan gwamnatin Najeriya da shugabanni a cikin 2020.

Najeriya dai ta kara nutsawa cikin kogin rashawa da ramin cin hanci, inda ta kara nausawa kasa cikin rijiyar cin hanci har da karin gaba uku, daga iyar zurfin da ta ke a cikin kafin 2020.

Sabon jadawalin cin maki tsakanin kasashe masu karancin satar kudade ya nuna cewa Najeriya ta samu maki 25 bisa 100 kacal a cikin 2020, wato kasa da maki 26 da kasar ta samu a kididdigar 2019.

Najeriya ita ce kasa ta 149 a jerin kasashen da ba a satar kudaden gwamnati, daga cikin kasashe 180.

Amma kuma a cikin 2019, Najeriya ce kasa ta 146.

A cikin 2018 kuma Najeriya ta zo ta 144.

CPI na dora kasashen duniya 180 a kan sikelin malejin satar kudaden gwamnati, ba wai a kan ra’ayoyin jama’a ko masana ko manyan ‘yan kasuwa ba.

Rahoton ya nuna kasashen Denmark da New Zealand ne kasashen da aka fi sauran kasashe rikon kudaden gwamnati bil-hakki da gaskiya.

Daga su kuma sai Finland, sai Singapore da Sweden da kuma Switzerland.

Kasashe irin su Sudan ta Kudu da Somalia, wadanda yaki ya durkusar, su ne na sahun farko na lalatattun kasashe.

Sai dai kuma a duk shekara gwanatin Najeriya na yi fatali da jadawalin yadda ake dora Najeriya a sahun maciya rashawa a duniya.

Mahukuntar kasar na ganin cewa gwamnatin Muhammadu Buhari ta na matukar kokari wajen dakile cin hanci da rashawa.

Karya Kungiyar TI Ke Wa Najeriya –Garba Shehu

Shehu ya ce gwamnatin Buhari ta cancanji yabo, jinjina da karin karfin guiwa wajen yaki da cin hanci da rashawa.

“Mu na kokarin gano daga inda Tranparency International ta samo bayanan ta, domin dai a sanin mu kungiyar cewa ta yi rahoton CPI ban a ta ba ne, ba ta tattaro bayanai da kan ta.”

“Nan da ‘yan kwanaki kadan Bangaren Tattara Bayanan Gwamnati (TUGAR) za ta sanar da jama’a yadda Kungiyar TI ta samo wannan bayani na ta.”

Amma dai Shehu ya kara da cewa rahoton karya ce kawai da soki-burutsu.

Ya kara da cewa mun sha kalubalantar rahoton da TI ke bugawa kan karairayin da ta ke wa Gwamnatin Najeriya, amma a karshe sai su kasa fitowa su kare kan su da hujjoji.

Share.

game da Author