Wani babban likitan kwakwalwa Philip Njemanze ya gargadi gwamnatin Najeriya ta kula matuka sannan ta yi karatun ta natsu kan kokarin siyo maganin rigakafin Korona da ta ke kokarin domin ‘yan kasar nan.
” Yakamata gwamnatin Najeriya ta yi watsi da shirinta na sayen alluran rigakafi daga kamfanonin hada magunguna da kuma mai da hankali kan ba da maganin na Ivermectin wa ‘yan Najeriya,”
Da yake jawabi a wani taron tattaunawa mai taken ‘Bayani don kwararrun kiwon lafiya da kuma kafofin watsa labarai a kan allurar rigakafin Pfitzer / BioNTech COVID-19 a ranar Juma’a, Njemanze ya ce akwai bukatar gwamnati ta dauki matakan shawo kan cutar ta hanyar ba da magungunan da za su taimaka wa jiki yakar cutar da rage kwayar cuta.
Ya kara da cewa maimakon kashe kudade kan allurar rigakafin, ya kamata Gwamnatin Tarayya ta ba Ivermectin fifiko wajen magance cutar a musamman ‘yan kasar nan.
Ivermectin shine ya fi dacewa mu maida hankali wajen amfani da shi tukunna tunda farko.
Abinda ya kamata a kula dashi shine ita Koronan ma tana rikidewa ne fa lokaci lokaci, idan aka bada rigakafin Pfitzer cutar ta rikide kwai fa babban kalubale kenan fa, za afada cikin rudani kenan.
Har yanzu ba mu san wani irin rashin lafiya mutum zai afka ciki ba a idan an yi rigakafin Korona din, tun da ba mu sani ba, dole ne mu ci gaba da yin taka tsan-tsan, dole a yi gwaji na asibiti na gaske a tabbatar zai yi wa mutanen mu aiki tukunna, don ba za mu yarda da surutan masu hada maganin ba tunda ota cutar idana ka yi mata rigakafi ma rikidewa take yi, maganin ya daina aiki sai kuma a fada halin ha-ula-I.
Kwararren masanin kiwon lafiyar ya gargadi gwamnatin Najeriya da kada ta rika dogaro da gwajin da aka yi a Amurka, ta gudanar da gwaji a asibiti a Najeriya saboda kasancewar allurar rigakafin da aka yi a Amurka ba tana nufin za ta yi aiki a Najeriya ba.
Da yake magana kan kudin maganin, farfesan ya ce gwamnatin Najeriya zata iya kashe dukkan kasafin kudin fannin kiwon lafiya na shekaru 10 zuwa 11 masu zuwa a kan allurar rigakafin ta Korona idan ba dakatar da ita aka yi ba tunda wuri.
” Gwamnati ba ta da wani dalilin kashe irin wadannan kudade wai don siyo rigakafin Korona din. A raba wa ‘yan Najeriya Ivercmicine tunda yana aiki ya fi mai makon amfani da Pfitzer wanda idan ba a manta ba sun taba shigo mana da rigakafi a 1996 wanda kowa ya san illar da ta yi wa’ yan Najeriya.
Discussion about this post