Ma’aikatan Hukumar yin Katin ɗan Kasa (NIMC) sun fara yajin aiki a fadin kasar nan.
Shugaban kungiyar ma’aikatan hukumar NIMC, Lucky Michael ya tabbatar da haka wa PREMIUM TIMES fara wannan yajin aiki da ma’aikatan ta ta ke yi.
Michael ya ce yajin aikin ya hada da duka ma’aikatan dake mataki ƴan na 12 zuwa ƙasa. Ya ce daga ranar bakwai ga Janairu wadannan ma’aikata da ke wannan mataki zuwa kasa ba za su yi aiki ki ba har sai an biya bukatun su.
Idan ba a manta ba gwamnati ta umarci ƴan kasa su je su gyara layukan wayoyinsu ta hanyar hada katin zama dan kasa da layin wayar su zuwa 9 ga Faburairu.
Wannan lamari ya haifar da cinkoson jama’a a wuraren yin katin ɗan ƙasa.
Ma’aikatan da suka zanta da manema labarai sun shaida cewa suna matukar wahala a wajen aiki.
” Babu kula daga shugabannin mu. Ba tun yanzu ba muna dai yi aiki ne kawai don a samu abin yi amma s babu kula ko kadan.