• PREMIUM TIMES |
  • Tallata Hajar ka |
  • Adireshin mu |
  • PTCIJ |
  • Dubawa
Premium Times Hausa
  • Labarai
    • All
    • Duniya
    TAKARAR SHUGABAN KASA: Muna tare da kai a koda yaushe – Sarkin Katsina Abdulmumini ga Osinbajo

    TA KICIME A APCn KADUNA: Ɓangaren Sha’aban ba su amince da zaben wakilan jam’iyyar APC da aka yi ba

    Yadda sojoji suka cafke gogarman masu garkuwa da mutane da wasu 150 a dazukan Zamfara da Katsina

    Askarawan Najeriya sun kashe ƴan bindiga 42, sun kama 20 sannan sun ceto mutum 63 da aka yi garkuwa da su – DHQ

    Yadda Tinubu ya taimake ni na zama gwamnan Jigawa -Badaru

    Crisis in Jos

    BAUCHI: Matasa sun babbake gidaje da shaguna da dama a Warji bayan Rhoda Jatau ta yi kalaman ɓatanci ga Annabi SAW

    GUDUN YIN BIYU-BABU: Gwamnan Bauchi ya sayi fam ɗin sake yin takarar gwamna, daidai lokacin da ya fito takarar shugaban ƙasa a PDP

    Farin jinin Buhari da mara min baya da yayi ya sa na samu daukaka a siyasa – Bala Mohammed

    Kano State Assembly

    Dan majalisar dokoki na jihar Kano ya doka ‘Ribas’ bayan ya tsunduma lambun jam’iyyar NNPP, ya ya rungumi tsintsiyar sa ya dawo APC

    Yadda EFCC ta damke Akanta Janar din Najeriya bisa zargin harkallar naira biliyan 80

    Dalilin da ya sa Buhari ya dakatar da Akanta Janar ɗin da ake zargi da kantara satar naira biliyan 80

    Nigerian Pilgrims

    HAJJIN BANA: Duk wanda ya zarce shekaru 65 bashi ba Hajji bana – Hukumar Alhazai

  • Labarai daga Jihohi
  • Wasanni
    CHAMPIONS LEAGUE: Ko dai tsinuwar Yaya Toure ta yi tasiri kan Pep Guardiola?

    PILLARS SUN KIRA RUWA: Daga yanzu a Abuja za su rika wasan gida kuma an zaftare musu maki 3

    Yadda Kanawa suka yi ragaraga da motar ƴan  Katsina United saboda Pillars ta buga kunnen doki a Kano

    GHANA vs NAJERIYA: Ko Najeriya za ta kauce wa ɗauko buhun kunya na 26 a hannun ‘Black Stars’?

    Barcelona ta yi wa Madrid dukan kabarin kishiya, ba sani ba sabo ta zura mata kwallaye 4 babu ko ɗaya

    ‘CHAMPIONS LEAGUE’: Yadda Benzama ya ceto Madrid daga rijiya gaba dubu, ya kori PSG kuma ya dawo da martabar sa a duniyar ƙwallo

    YAƘIN UKRANIYA YA CI ƘUNGIYAR CHELSEA: ‘Zan sayar da kulob ɗin na sadaukar da kuɗin ga tallafin waɗanda yaƙin Ukraniya ya kassara’ -Abramovich, mai ƙungiyar kuma ɗan asalin Rasha

    RASHA: FIFA da UEFA sun dakatar da ƙungiyoyin Rasha buga wasannin ƙwallon Turai da duniya baki ɗaya

    KYAUTAR NAIRA MILIYAN 2: Allah ya saka wa Ahmed Musa, ina kira ga ‘yan wasa na yanzu su yi tattali don gaba – Obiekwue

  • Kiwon Lafiya
  • Nishadi
  • Bidiyo da Hotuna
    KURUNKUS: Malami ya fito takarar gwamnan Kebbi, ya ce jama’ar jihar ne suka tilasta masa ya fito

    2023: Ɗan takarar shugaban kasa, Rotimi Amaechi ya ziyarci masarautar Dutse

    LABARI CIKIN HOTUNA: Yadda ƴaƴan jam’iyyar APC da dubban mutanen Kaduna suka yi wa Sanata Uba Sani goma ta arziki

    BIDIYO: Shin zaka iya zama da mai dauke da cutar Kanjamau? – Ra’ayoyin mutane

    Dalilin da ya sa muka yi tattaki har Dubai domin taya Aisha Buhari murnar zagayowar ranar haihuwar ta – Matan Gwamnonin Najeriya

    BIDIYO: Yadda ‘yan bindiga suka rika jibga ta kafin a biya naira 50,000 kudin fansa – Dattijo Saidu Dabo

    ‘Yan mata marasa aure sun fi matan aure amfani da magungunan takaita Iyali – Ma’aikatar Lafiya

    BIDIYO: Kwalaben ruwan maganin rigakafin Korona sama da Miliyan daya da aka lalata a Abuja saboda sun gama aiki kafin a dirka wa ‘yan Najeriya

    BIDIYO: RIKICIN BILLIRI: Yadda muka rasa ‘yan uwa da dukiyoyin mu a rikicin sarauta – Galadiman Tangale

No Result
View All Result

KUSHEWAR BADI SAI BADI: Siradi 10 Da ’Yan Najeriya Su Ka Tsallake Kafin Shiga 2021

Ashafa MurnaibyAshafa Murnai
January 1, 2021
in Babban Labari, Rahotanni
0
Mutum 9 cikin 10 a jihohin Sokoto, Taraba da Jigawa fakirai ne tuburan – Rahoton NBS

Bayyanar cutar Korona a karon farko a Najeriya a ranar 27 Ga Fabrairu, ya gigita kasar nan. Ga duk dan Najeriya ya fahimci cewa akwai wani babban lamari kuma mummuna da ke neman mamaye duniya, ba ma Najeriya kadai ba.

Watan Maris na shigowa al’amurra su ka murde wa Najeriya, su ka dagule, su ka daburce su ka damalmale. Ya zuwa ranar 27 Ga Maris, 2020, tuni ’yan Najeriya sun fara gudun kowa ta sa ta fisshe shi, saboda sanarwar za a kulle wasu jihohi, musamman Lagos da Abuja, sakamakon fantsamar da cutar korona ke kara yi.

Mako daya bayan wannan, sai kasa ta dagule, arankatakaf din ta. Daga labarin kulle tashoshin jiragen sama, sai labarin kulle tashoshin ruwa. Sai batun kulle Lagos da Abuja. Sai hana zirga-zirgar motoci. Sai dokar kulle mutane su na zaman gida tilas. Sai kulle masallatai da coci-coci, kasuwanni da wuraren cin abinci da na shakatawa.

Tun daga nan milyoyin jama’a su ka shiga kuncin rayuwar da har yau idan wasu sun fita, to wasu ba su fita daga kuncin ba.

Yayin da ’yan Najeriya masu tsawon rai su ka kai ga shiga shekarar 2021, ko tantama babu za a iya kiran waccan da aka tsallake, wato 2020, shekarar da kyar na sha ya fi da kayar aka damke ni. Dalili, ai ba cutar korona kadai ce manyan kalubalen da su ka dabaibaye kasar ba.

Abin ne da yawa, wai ‘mutuwa ta je kasuwa’. Amma dai ga wasu muhimman siradan da ’yan Najeriya su ka tsallake kafin su shiga shekarar 2021.

Cutar Korona: Allah kadai ya san yawan mutanen da korona ta kashe a duniya, baya ga wadanda alkaluman kididdiga su ka bayyana. A Najeriya mutane da yawa na su zuwa gwaji. Wani ya kamu da cutar ya warke, wani kuma ta kama shi ya bingire. Mace-mace da dama ba a fito an bayyana musabbabin su ba.

Sai dai kawai inda mutum zai kara firgita, idan ya ga fitattu ko mashahuran ‘yan Najeriya da cutar ta kashe a cikin 2020.

Korona ta kashe majiyyaci ta kashe mai jiyyar sa. Ta kashe dimbin jami’an kula da llafiya, kuma ta kama dubbai a kasar nan.

Mutanen da su ka mutu ba ta musabbabin cutar korona ba, su na da dimbin yawa. Duk wanda ya ga jerin wasu mashahurai ‘yan asalin Jihar Jigawa da su ka bar duniya cikin 2020, tabbas abin zai tabbatar masa da cewa duk wanda ya tsallake 2020, ya cancanci a kira shi mai rabon ganin badi. Ko a Jajibirin sabuwar shekara, wato ranar 31 Ga Disamba, 2020 an yi rashin mahaifin tsohon Ministan Harkokin Waje, dan asalin Jihar Jihar Jigawa, Nuraddeen Mohammed.

Boko Haram: Cikin shekarar 2020 dai Boko Haram ba su jefa bama-bamai sosai ba. Amma fa sun yi mummunan kisa. Su tare hanya su kashe. Su yi wa garuruwa tattaki su kashe na kashewa. Su kai wa sojoji hari su kashe na kashewa. Ba sau daya ba sun kashe sama da mutum 30 ko 40 a lokaci guda.

Bala’in ta’addancin Boko Haram na ci gaba da karuwa a jihar Barno, la’akari da cewa ta’addancin ya koma reshe biyu, wato bangaren tantagaryar ‘yan Boko Haram, su Shekau da kuma rundunar ‘yan ta’addar ISWAP masu rassa a wasu kasashe, amma duk buri daya su ke neman cimmawa su da su Shekau din.

Su kan su Hukumomin Tsaro na Sojojin Najeriya sun bayyana cewa cikin watanni 10 na 2020, wato tsakanin Maris zuwa Disamba, Hukumar Tsaro ta Sojojin Najeriya ta tabbatar da cewa a cikin shekarar 2020, tsakanin ranar 18 Ga Maris zuwa 30 Ga Disamba, sojoji sun ‘markade’ tantagaryar mabarnata 2,403 a fadin kasar nan.

“Baya ga wadannan masu laifi 2,403 da aka ‘makade’, Enenche ya kara da cewa a yankin Arewa maso Yamma an kwato dabbobi 5,281 da kuma albarusai 6,951 sai kuma bindigogi 120 masu samfuri daban-daban daga hannun ’yan bindiga.

“Banda wadannan kuma akwai wasu ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga da dama wadanda aka ‘narkar’ da su a hare-hare ta amfani da jirayen yaki.” Inji Enenche.

Ya kuma yi bayanin cewa a cikin wadannan watanni 10, sojoji sun ceto mutane 864 da aka yi garkuwa da su a jihohi daban-daban a fadin kasar nan.

Daga wadannan bayanai, mai karatu zai tabbatar da cewa ba a ma san iyakar rayukan da aka kashe cikin Najeriya a shekarar 2020 ba.

Garkuwa Da Mutane: Da Kyar Na Tsere Ya Fi Da Kyar Aka Damke Ni

Bala’in da Najeriya ta tsinci kan ta dalillin buwayar masu garkuwa da mutane, ya ma sa ba’arin milyoyin al’ummar kasar nan sun daina jin tsoron cutar korona. Abin da ya fi damun su a yanzu shi ne yadda masu garkuwa su ka fi karfin hukuma.

A kullum idan Boko Haram ba su kama matafiya sun yi garkuwa da su ba, to ‘yan bindiga za su tare hanya su kwashi matafiya su nausa cikin daji da su.

Har yau ba a kididdige yawan jama’ar da aka yi garkuwa da su a jihohin Kaduna, Katsina, Zamfara, Sokoto, Neja da sauran jihohi ba. Ba a kuma san adadi ko naira bilyan nawa masu garkuwa su ka karba a matsayin kudin fansa a cikin 2020 ba.

Sun buwayi kauyuka sun buwayi garuruwa. Sun buwayi dazuka sun buwayi manyan titina. Ta kai a yau ka tambayi dan Arewa ya shaida maka abin da ya fi tsoro, tashin farko zai ce maka masu garkuwa da mutane.

Babab mutum komai mukamin sa, ce maka zai yi ya fi jin tsoron bin hanyar Kaduna zuwa Abuja. Gwamna na tsoron bin hanyar haka sarki. Jami’an tsaro na tsoron bi, haka su ma malamai. Talaka na tsoro haka attajiri.

Cikin karshen shekarar nan ne fa aka yi garkuwa da dabilai jimlar 423 a Jihar Katsina. Yayin da Boko Haram su ka kassara Arewa maso Gabas, su kuma masu garkuwa sun kassara yankunan Arewa maso Yamma musamman Katsina, Sokoto, Zamfara, Kaduna da Neja.

Allah kadai ya san yawan wadanda aka yi garkuwa da su a cikin 2020. Kuma da yawa sun mutu a hannun masu garkuwa, an bindige su bayan an kai kudin fansa, ko kuma bayan an kasa kai kudin fansa.

Shi kuwa wanda ya kubuta daga hannun masu garkuwa da kuma wadanda ke addu’a kada Allah ya sa su da masu garkuwa su ga juna, za a iya cewa sun tsallaka cikin 2021 a halin da Bahaushe ke cewa, ‘da kyar na tsere, ya fi da kyar aka kama ni.’

Tsadar Rayuwa: Shekarar 2020 ta haifar wa ’yan Najeriya da tsananin kuncin rayuwa. Wasu dalilan sun hada da Hare-haren Boko Haram masu kashe mutane, su kwashe dukiyoyin su, sai masu garkuwa da ke karbe ilahirin dukiyar mutum da ta dangin sa kafin su sake shi. Da yawa ma gidajen su ake sayarwa a biya masu garkuwa kudin. Ga kuma dabbobi da kayan abinci da masu garkuwa ke kwashewa jama’a.

Da yawan mutanen kauye sun samu damar tsallake siradin 2020 su ka tsallako 2021 a yau, saboda sun yi hijira daga kauyukan su sun koma birane da zama. Saboda tsoron ’yan bindigar da su ka gagari gwamnati.

Akwai kuma dalili na game-gari, wato kullen zaman gida tilas da aka yi na tsawon watanni sakamaon fantsamar cutar korona.

Karyewar tattalin arziki a lokacin korona, ta yadda har sai da ta kai farashin gangar danyen man fetur a kasuwannin duniya ya koma daidai da farashin ruwan askin cikin kofin wanzami. Wannan ma ya haifar da matsalar karayar tattalin arziki.

Zaman dirshan da aka rika yi a gida ya haifar da fitintinu, musamman bas ace-sace da yi wa cin zarafin mata.

Tsadar Kayan Abinci:

Hana shigo da kayan abinci daga kan iyakokin Najeriya da kullle kan iyakokin sukutum ya haifar da matsanancin tsadar abinci. A cikin 2020 sai da ta kai shinkafar da ake nomawa a cikin kasa ta gagari talaka. Duk abin da ka taba za ka ji ya yi tsada. Kwanon shinkafar da aka sayarwa naira 500 kafin hawa mulkin Buhari, yanzu haka har ranar jajibirin shiga 2021 naira 1500 ake sayar da shi.

Saura nau’ukan kayan kayan abinci irin su gero, garin kwaki, masara, wake, dawa sun yi tsada matuka. Aka wayi gari akusan karshen 2020, sai da albasa ta nemi gagarar hatta masu karfin su kan su. Buhun da a da ake sayarwa naira 17,000, sai da ya dangana da naira 47,000, wasu jihohin ma har naira 50,000.

Gidajen da aka shekara 20 ba a ci shinkafar Hausa ba, sai ga shi sun shafe shekarar 2020 ba su ci shinkafar Thailand mai kyau ko da a rana day aba. Farashin buhun shinkafa ya zama kudin jarin fara wata sana’a mai kwari.

Yayin da gwamnatin Buhari ke bai wa masu karamin karfi tallafi na lamunin jarin naira 20,000 domin kama sana’a, kwata-kwata kudin bai kai kudin buhun shinkafa ba.

Shi kan sa Shugaba Buhari ya san ana cikin halin matsi da kuncin rayuwa sanadiyyar tsadar kayan abinci. Domin ko a cikin makon karshe na shekarar 2020, ya sha aradun cewa zai magance tsadar kayan abinci cikin 2021 a kasar nan.

Tsadar Man Fetur: Kuncin rayuwa da aka shiga cikin 2020 bai hana gwamnati rika kara wa litar man fetur kudi ba. har sai da ya dangana da naira 167. Ba fetur kadai aka kara wa kudi ba. Ita ma wutar lantarki an kara mata kudi. Wannan lamari ya bai wa kowa mamaki da kuma al’ajabi, ganin yadda Gwamnatin Buhari ta rika karin kudin fetur a lokacin da ake cikin halin kuncin tsadar rayuwa.

2020: Shekarar Takunkumi: Wannan shekara dai ta karya alkadarin wata karin magana da Bahaushe ke cewa, ‘takunkumi sai kura!’ Annobar korona ta sa a duniya kaf an koma daura takunkumi a baki da hanci. Tun kafin watan Maris ya yi nisa tuni takunkumi ya mamaye biranen kasar nan. Kowa ka gani daure da takunkumi, tamkar kura a hannun gardi. A yau ta kai ta kawo tun Shugaba Buhari ba ya daura takunkumi, har ta kai yanzu ta kai shi ga daurawa tilas.

A karshen 2020 ma abin ya yi zafi sosai, har gwamnatin Jihar Kaduna da Gundumar Babban Birnin Tarayya Abuja, sun fara cin tarar naira 20,000 ga duk wanda ya fito bai daura takunkumi a bakin sa ba.

Shekarar 2020 ta hana abubuwa da yawa. Ta hana zumunci, ta hana musabaha hannu da hannu. Har yau Buhari ba ya gaisawa da kowa, sai dai su hada damtsan hannaye, kamar ‘yan dambe. Wannan ita ce sabuwar nau’in gaisawar da aka tsallako cikin 2021 da ita.

2020: Shekarar Cinikin Mutum Kamar Cinikin Akuya A Kasuwa:

A wannan shekara ce masu garkuwa da mutane su ka fi cin kasuwar cinikayyar mutanen da su ke kamawa. Yadda ake cinikin wata babbar kadara, haka ake ciniki tsakanin dangin wanda aka kama da masu garkuwa. Idan ba su sallama ba, a bar cinikin sai gobe idan an kara taya wa. Ba a taba ganin irin wannan bala’i kamar cikin 2020.

Shi ya sa ake ganin masu garkuwa da mutane sun fi karfin gwamnati, domin har zaman sulhu da neman sassauci gwamnatin ke yi da su.

2020: Shekarar Karin Karin Haraji: Cikin wannan shekara haraji nau’I daban-daban ya karu. Kuma an kirkiro wasu. Duk wannan ya faru ne saboda rashin kudade a hannun gwamnati. Harajin-jiki-magayi (VAT) ya karu. An kirkiro harajin ladar-ganin-ido, wanda ko kadara mutum zai sayar, sai ya fitar wa gwamnatin tarayya haraji a cikin kudin. Ga kuma harajin-la’ada-waje, wanda ko haya mai gidan haya ya bayar da gidan sa, sai ya cire wa gwamnatin tarayya haraji a cikin kudaden.

Kasancewa Kasafin 2021 na naira tiriliyan 13.588 ya zama riwayoyin da bas u da tabbas, domin babu kudin babu alamar su, a ranar karshe ta 2020 Buhari ya gargadi Shugabannin Hukumomin Tara Kudaden Haraji cewa duk wanda bai tara kudi daya a 2021 ba, to zai tara masa gajiya.

Shekarar 2020 ta zama shekarar da a tarihin kasar nan aka fi ciwo bashi daga kasashen waje.

Kuma wannan shekara ta 2020 ta zo da ibtila’in Tarzomar #ENDSARS, wadda tun bayan yakin Basasa ba a taba yin tarzomar da ta haifar da asarar dukiya kamar ta ba.

Ita kan ta kasar ta shiga tangal-tangal a cikin 2020, domin kadan ya rage da tarzomar #ENDSRARS ya tarwatsa ta. Watakila da a cikin 2021, sai dai a bayar da wani labarin daban, ba irin wannan ba.

Yayin da ’yan Najeriya su ka shiga 2021, babu mai fatan sake maimaita abubuwan da su ka faru cikin 2020.

Tags: AbujakoronaLabaraiNajeriyaPREMIUM TIMES
Previous Post

KORONA: Legas, Abuja da Kaduna suka fi yawan wadanda suka kamu ranar Jajibarin 2021 cikin mutum 1,031 da suka kamu

Next Post

2021: Shekarar kawo karshen da matsalolin da suka zame mana kashin kifi a wuya – Buhari

2021: Shekarar kawo karshen da matsalolin da suka zame mana kashin kifi a wuya - Buhari

Binciko

No Result
View All Result
Karanta

Ramadan Kareem AD

Sabbin Labarai

  • Ƴan sanda sun kashe masu garkuwa da mutane uku a Adamawa
  • Dalilin da ya sa za mu ƙirƙiro gundumomi 268 a jihar Filato – Lalong
  • TAKARAR SHUGABAN KASA: Muna tare da kai a koda yaushe – Sarkin Katsina Abdulmumini ga Osinbajo
  • TA KICIME A APCn KADUNA: Ɓangaren Sha’aban ba su amince da zaben wakilan jam’iyyar APC da aka yi ba
  • Rundunar ƴan sandan Kano ta kama wata moto cike makil da kayan haɗa nakiya, harsasai da bindigogi

Abinda masu karatu ke fadi

  • Google on Masarautar Kano: Hassada Ta Sa Wasu Na Neman Wofintar Da Kokarin Su Danfodiyo! Daga Imam Murtadha Gusau
  • Kuşburnu Çekirdek Yağı on Dalilin da ya sa muka yi sallar Idi ranar Laraba a Bauchi, muka ki bin sanarwar Sarkin musulmi – Sheikh Dahiru Bauchi
  • Google on HARKALLAR BILIYAN 3.6: Ba nine Balan da ke jerin sunayen masu mallakin kamfanin Adda ba – Gwamna Bala
  • Google on SIYASAR ZAMFARA : Maitaimakawa tsohon dan takarar gwamna a APC akan harkar jarida ya sauya sheka
  • Google on RAMIN MUGUNTA: Yadda Boko Haram suka afkawa bam din da suka dana wa Sojojin Najeriya

Fanni

Tweets by PTimesHausa
  • All Homepage Blocks
  • Home
  • Home
  • Main Home

© 2022 JNews - Premium WordPress news & magazine theme by Jegtheme.