Kungiyar Miyetti Allah ta amince da bin dokokin gwamnonin jihohin Yarabawa, ciki harda hana kiwon dare

0

Bayan tashi daga taron da gwamnonin yankin Yarabawa da kungiyar Miyetti Allah suka yi a garin Akure ranar Litinin, kungiyar ta yarda daga yanzu makiyaya su dai na yin kiwon dare a fadin yankunan jihohin Yarabawan.

Bayan haka kuma MACBAN ta amince daga yanzu yaron da bai kosa ba wato bai kai munzalin ya rika fita kiwo ba kada su rika kiwo.

Sannan kuma sun ce lallai suma hare-haren ‘yan bindiga ya addabe su wanda ya sa zargin da ame musu bai kamata a rika yi ba.

Su kansu jami’ an tsaro shaida ne cewa tare da zun sun sha fita farautar ‘yan bindiga da mahara kuma suna ba su kyakkyawar goyon baya da gudunmawa.

Shugaban kungiyar MACBAN, Muhammadu Kirowa ya kara da cewa a shirye kungiyar ta ke ta ci gaba da bada gudunmawarta wajen ganin an kawo karshen hare-hare da garkuwa da mutane.

PREMIUM TIMES ta buga yadda wani shugaban matasa mai suna Sunday Igbolo ya bada irin wannan wa’adin korar Fulani makiyaya a Jihar Oyo, abin da ya haifar da tashin hankalin da har aka kona gidaje da dukiyoyin Sarkin Fulanin Oyo.

Tuni da Sufeto Janar na ’Yan Sanda Mohammed Adamu ya bada umarnin a yi bincike.

Yayin da wasu lauyoyi su ke ganin cewa Sunday ba shi da ‘yancin korar Fulanin, matasan yankin na cewa su na da ‘yancin kare kan su.

PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda Miyetti Allah sun nemi a kamo Sunday Igboho mai rura fitinar korar makiyaya.

Kungiyar Kare Muradin Fulani Makiyaya, Miyetti Allah, ta yi kira a gaggauta kama dan rajin kafa kasar Yarabawa mai suna Sunday Igboho.

Shugaban Kungiyar Fulani Makiyaya ta Miyetti Allah na Jihar Oyo, Ibrahim Jiji ne ya bayyana haka ga manema labarai a Ibadan babban birnin Jihar, inda ya kara hakkakewa cewa Fulani makiyaya fa ba mabarnata ba ne.

“Dukkan mu dai ‘yan Najeriya ne. Mu na kaunar kokarin da Gwamnan Jihar Oyo Seyi Makinde ke yi wajen fitowa karara ya na fadin gaskiya. Mutanen ba su zaune lafiya, su na cikin tashin hankali, wasu ma sun gudu sun bar gidajen su.

“Mu na so a yi wa Sarkin Fulani adalcin dangane da barnar da aka yi masa a gida. Dukkan wadanda su ka yi masa barnar kona masa gidaje da dukiyoyi dole a kama su a hukunta su. Saboda ba su fi gwamnati karfi ba. Wane ne Sunday Igboho, kuma ta yaya aka yi har ya fi karfin gwamnati?

“Na sha fada cewa a cikin kowace kabila akwai mabarnata, ba wai sai a cikin Fulani kadai ba. Wadanda a yanzu ake gallazawa ba su ne masu laifin da ke addabar jama’a din ba. Wadanda ake kora a yanzu su ne fa ke zaune alfiya da mutane. Ya kamata gwamnati ta yi dukkan kokarin da za ta yi domin ta tabbatar zaman lafiya ya dawo a yankin Ibarapa.”

Shi dai Igboho shi ne ya ja zugar wasu matasa su ka kai wa Fulani farmaki a Ibarapa.

Sai dai kuma Kakakin Fadar Shugaban Kasa Garba Shehu, ya ce Shugaba Muhammadub Buhari ya umarci Sufeto Janar na ‘Yan sanda Mohammed Adamu ya sa a kama Sunday Igboho.

Sai dai kuma Kakakin Yan sandan Najeriya Frank Mba da na Jihar Oyo Olugbengba Fadeyi ba su amsa kiran PREMIUM TIMES ba, domin jin inda aka kwana.

Za A Yi Bala’i A Kasar Nan Idan Aka Kama Igboho –Matasan Yarabawa.

Tuni da Yarabawa su ka tashi haikan a kungiyance su na cewa idan aka kama Sunday Igboho, to za a yi bala’i a kasar nan.

Haka shugaban kungiyar Matasan Yarabawa Olalekan Hammed ya bayyana.

Ya ce matasan yankin Ibarapa da ma wasu matasana Yarabawa ba za su bari a kama dan uwan su ba.

Share.

game da Author