Gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje ya yi kira ga kungiyar daliban jami’o’i su kafa askarawan tabbatar an kiyaye dokokin korona a jami’oin su.
Ganduje ya ce wayar da kan dalibai sanin muhimmancin kiyaye dokokin gujewa kamuwa da cutar Korona zai taimaka wajen dakile yaduwar cutar a jihar Kano.
Gwamnan ya fadi haka ne ranar Lahadi da yake ganawa da shugabanin kungiyoyin dalibai na jami’o’in dake jihar.
Ya yi kira da su mara wa gwamnati baya a kokarin da take yi wajen dakile yaduwar korona a jihar.
A ranar 24 ga Janairu PREMIUMTIMES ta buga labarin kafa sabuwar kungiyar duba gari don tabbatar da an kiyaye dokokin korona a jihar.
Ya ce gwamnati ta yi haka ne domin a tilasta wa mutane bi da kiyaye dokokin korona a fadin jihar.
Ganduje ya ce za a kafa wannan kungiya ta hadin gambiza ce, wanda zai hada da jami’an ‘yan sanda, Sibul Difens da wasu da za a dauka domin tabbatar an yi nasara a wannan aiki.
Ya mika godiyarsa ga masu makarantu masu zaman kansu kan yadda suke kokarin taimakawa gwamnati wajen kiyaye dokar Korona.
Ganduje ya yi alkawarin yin kari a kudaden da gwamnati ke tallafawa karatun dalibai na jihar.
Ya yaba yadda daliban ke zaman lafiya a jami’o’i su amma ya hore su da su nisanta kansu daga ta’ammali da muggan kwayoyi da shiga kungiyoyin asiri.
Ganduje ya ba kowani shugaban kungiyar daliban jami’oin dake jihar kyautar takunkumin fuska 100,000 su rarraba a makaranta.
Shugaban kungiyar daliban jihar Kano na ƙasa NAKSS Yahaya Kabo ya jinjina kokarin da gwamnati ke yi wajen dakile yaduwar cutar sannan ya gode wa gwamna da kyautar da yayi musu na takunkumin fuska.