Wata Kotun Majistare da ke Abuja babban Birnin Tarayya, ta bada umarnin maida mawallafin Sahara Reporters hannun jami’an bincike na ’yan sandan FCIB, ba tare da amincewa ta bada belin sa ba.
A ranar Talata ne dai aka maida Sowore kotu, bayan tura shi kurkukun Kuje da aka yi a ranar Litinin, kafin a duba yiwuwar beli washegari Litinin din.
Mai Shari’a ya sake dage sauraron belin zuwa ranar Juma’a, 8 Ga Janairu.
An dai kama Sowore ne a ranar jajibirin shiga shekarar 2021 a lokacin wata zanga-zangar lumana a Abuja.
An kama shi ne tare da wasu mutum hudu a wurin zanga-zangar, wadda ya yi zargin cewa an ci masa zarafin da har aka ji masa ciwo, aka fitar masa da jini a karan hancin sa.
Kafin a tura shi kurkukun Kuje inda ya kwana daya, Sowore ya shafe kwanaki hudu a ofishin ’yan sanda, inda sai a ranar Litinin su ka kai shi kotun Majistare ta Zone 2.
Ana zargin sa da shirya makarkashiya da kuma kokarin tunzira jama’a su tayar da fitina.
Mai Shari’a Maibel ta ki bada belin sa, amma kuma bayan ta saurari bangarorin biyu, ta ce kada a maida shi kurkuku, a kai shi hannun ‘yan sandan bincike na FCID da ke Area 10, Abuja.
Markabu Tsakanin Sowore Da Jami’an Kurkuku A Kotu
Bayan an fito kotu dai an yi markabu tsakanin jami’an gidan kurkuku, wadanda su ka nemi Sowore ya shiga motar su a tafi, amma ya ki shiga, ya ce yanzu a hannun ‘yan sanda ya ke, ba hannun jami’an kurkukun Kuje ba.
An nemi a tayar da rincimi yayin da Sowore ya ki yarda jami’an kurkuku su tafi da shi cikin motar su.
Daga nan ya danna, ya sake komawa cikin kotu ya zauna. Zaman sa ke da wuya babban jami’in kurkukun ya biyu shi ya na lallashin sa cewa ya tashi su tafi, ba za a cutar da shi ba.
“Oga, ka tafi kawai ka ba ni wuri. Ba ni da wata hulda da kai a yanzu. Kotu ta raba ni da ku, yanzu a hannun jamai’an ‘yan sanda na ke, ba a hannun jami’an kurkuku ba.
“Idan za ka ku tafi, to ku kama gaban ku kawai. Ba ni da wata magana da ku. Tsakani na da kai sai dai wata huldar can daban, amma ba ta shiga motar ku ‘Black Maria’ ba.” Inji Sowore.
Dama kuma kafin a kai ga markabun, Sowore bayan ya fito daga cikin kotu, ya shaida wa manema labarai cewa kurkukun Kuje bai bi umarnin da kotu ta bayar na a kula da shi Sowore da suran masu zanga-zangar su hudu ba.
Maimakon haka, Sowore ya bayyana cewa sai aka killace su kawai.
Ya yi ta cewa duk abin da gwamnatin Shugaba Buhari ke yi masa, ba za ta kashe masa guiwa ba, sai ma kara masa azama da ta ke yi.
Dama kuma a ranar Litinin gidan Kurkukun Kuje ya nemi ya ki karbar Sowore da sauran mutum hudun da aka tura su tare.
Wani ganau kuma dan rakiya ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa lokacin da ‘yan sanda su ka kai Sowore Kuje, jami’an kurkukun sun ki karbar sa, a bisa hujjar cewa babu wurin ajiyar su a ciki.
“An shafe sama da sa’o’i hudu ’yan sanda na ta kokarin kiran jami’an Hukumar Harkokin Cikin Gida, wadda a karkashin ta ne gidajen kurkuku su ke, domin ta sa baki a karbi su Sowore. Daga karshe dai wajen 9:30 na dare aka karbe su.” Inji majiyar mu, wanda ya tabbatar da a gaban sa aka yi komai.
Discussion about this post