Kotu ta daure dan acaban da ya yi wa wata jatuma fyade

0

Kotu a Ado-Ekiti ta daure wani dan acaba Olaleye Jimoh mai shekaru 29 da aka kama da laifin yi wata jatuma mai shekara 50 fyade.

Alkalin kotun Adefumike Anoma ta yi watsi da rokon sassaucin da Jimoh ya yi inda ta yanke masa hukuncin zama a kurkuku har sai an kammala yin shawara da bangaren da ke kula da irin wadannan laifuka.

Lauyan da ya shigar da karar Oriyomi Akinwale ya ce Jimoh ya danne wannan jatuma ne ranar 22 ga Janairu a kauyen Odo-Owa Ekiti dake karamar hukumar Ikole-Ekiti a lokacin da ta yi hayan sa ya kaita gonar ta.

Akinwale ya sahida wa kotu cewa kafin dan acaban ya kai ga isa gonar wannan jatuma sai ya kanke hanya, ya samu wani wuri da ciyayi suka yi rumfa ya yi mata fyade.

An dage ci gaba da sahri’ar zuwa 4 ga Faburairu.

Share.

game da Author