Babbar Kotu a jihar Kaduna ta bada umurnin a killace uwargidan shugaban kungiyar Shi’ah Ibrahim El-Zakzaky, Zeenat a wurin da ake killace wadanda suka kamu da Korona bayan bayyana sakamakon gwajin cutar da aka yi masa.
Alkalin kotun Gideon Kurada ya bada wannan umurni ne bayan lauyan dake kare El-Zakzaky da Uwargidansa, Femi Falana ya gabatar da sakamakon gwajin cutar da ya nuna cewa lallai Zeenat na dauke da cutar.
Falana ya ce a zaman da kotun ta yi ya gabatar da shaidu guda hudu wanda a ciki akwai likitocin da suka yi mata gwajin kuma suka tabbatar ta kamu da cutar.
Ya ce a dalilin haka ne ya roki kotu ta umarci mahukunta su killace Zeenat a wurin dake kula da wadanda suka kamu da cutar, saboda a inda ake tsare ds su a Kaduna babu asibiti ko wuri da za a iya duba ta da kyau.
PREMIUMTIMES HAUSA ta buga labarin yadda likitoci suka gano Zeenat ta kamu da cutar Korona din.
An buga cewa daya daga cikin ‘ya’yan Zeenat ne ya fara sanar wa duniya cewa lallai fa mahaifiyar sa ta kamu da Korona amma kuma anki a bata dama ta killace kanta da kuma samun magani.
Ko da yake a lokacin da yake zannan zargi ga mahukunta Kontirolan firsin din Kaduna ya bayyana cewa ba a sanar dashi sakamakon gwajin da aka yi wa uwargidan El-Zakzaky ba, saboda haka bashi da masaniya cewa wai ta kamu da korona ko bata kamu da cutar ba.