Shugaban hukumar kula da cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko NPHCDA, Faisal Shuaib ya bayyana cewa shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, mataimakinsa Yemi Osinbajo da manyan jami’an gwamnati za su yi allurar rigakafin cutar korona a talabijin domin duk mutane su gani a kuma shaida.
Faisal ya ce yin haka zai taimaka wajen karfafa guiwar mutane wajen amincewa da yin rigakafin kuma su yadda ayi musu alluran idan aka kammala shigowa da ruwan maganin rigakafin.
Ya kawo misalan yadda shugabanin kasashen duniya da suka hada da Joe Biden zababben shugaban kasar Amurka da Benjamin Netanyahu firaye ministan kasar Isra’ila da suka yi haka domin karfafa gwiwowin mutanen kasashen su kan amincewa da rigakafin.
Faisal ya ce da zaran Najeriya ta karbi maganin rigakafin za a fara yi wa shugabanin gwamnati, ma’aikatan lafiya, tsoffi da mutanen dake da gajiyayyu.
A ranar biyar ga watan Janairu PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin yadda Najeriya za ta karbi maganin rigakafin cutar korona na Pfizer da BioNTech 100,000 a karshen watan Janairu.
Kamfanin COVAX wanda ya dauki nauyin shigo da magungunan zai shigo da kwalaben maganin 100,000 sannan daga baya kamfanin ya kara shigowa da miliyan 42 na maganin a matsayin gudunmawar kamfanonin vaccine alliance da GAVI wa Najeriya.
Za a iya dakile yaduwar korona idan an yi wa akalla Kashi 70 daga cikin adadin yawan mutanen dake zama a ƙasa.
A dalilin haka gwamnati za ta fara yi wa Kashi 40 rigakafi a cikin wannan shekara 2021 sannan ta yi wa kashi 30 a shekaran 2022
gwamnati ta kafa kwamitin mutum 18 wanda za su tabbatar Najeriya ta samu maganin rigakafin cutar korona da zaran hukumomin lafiya sun amince da shi.
A kwanakin baya gwamnati ta yi wasu kwararrun ma’aikatan lafiya sun bayyana ra’ayoyin su wa PREMIUMTIMES cewa da wuya Najeriya ta fara yi wa mutane allurar rigakafi a watan Janairu ganin yadda kasashen duniya da dama ke layin samun a basu maganin don mutanen su.
Kwararrun sun kuma ce a yanzu haka Najeriya bata da wurin ajiyan wadannan magunguna koda an shigo da su kasan.
Sannan karamin ministan kiwon lafiya Olorunnimbe Mamora ya gargaddi mutanen kasar nan da su kara zage damtse wajen kiyaye sharuddan guje wa kamuwa da cutar korona musamman yanzu da babu tabbacin lokacin da kasan za ta samu maganin rigakafin.
Ya ce Najeriya ba za ta samu maganin rigakafin cutar ba a lokacin da ta tsayar ba wato karshe watan Janairu.