Korona ta kashe tsohon ministan Buhari a Abuja

0

An bada sanarwar mutuwar tsonon Antoni Janar kuma tsohon Ministan Shari’a, Abdullahi Ibrahim a ranar Lahadi.

Ibrahim ya rasu a Cibiyar Killace Masu Cutar Korona a Gwagwalada, Abuja.

Ibrahim ya kuma yi wa Buhari Ministan Sufuri da Harkokin Jiragen Sama a lokacin da Buhari ya yi mulkin soja, tsakanin 1984 zuwa 1985.

Wani babban jami’in gwamnatin da ba ya so a ambaci sunan sa, shi ne ya sanar da PREMIUM TIMES wannan rashin tsohon ministan da aka yi.

Sannan kuma wakilin mu ya duba shafin Ibrahim na Wikipedia, ya tabbatar da an yi sanarwar rasuwar ta sa a cikin shafin.

Ibrahim ya yi Ministan Shari’a a zamanin mulkin soja na Abdulsalami Abubakar, na watanni tara.

Shi ne Ministan Shari’ar da aka damka mulki a hannun farar hula na Olusegun Obasanjo tare da shi a cikin 1999.

Tun kafin a nada shi Ministan Shari’a, Ibrahim wanda dan asalin jihar kogi ne, ya yi Ministan Ilmi, Kimiyya da Fasaha.

Ibrahim shi ne babban mutum na baya-bayan nan da ya rasa ran sa sanadiyyar kamuwa da cutar korona.

Yanzu dai duniya baki daya na cikin damuwa da gaganiyar dakile cutar korona ta hanyar kokarin samarwa da yin allurar rigakafin cutar.

Sai dai kuma yayin da wasu kasashen tuni sun yi nisa wajen fara yin rigakafin korona, har yanzu ba a fara Najeriya ba.

Share.

game da Author