Shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya, gwamnan jihar Ekiti Kayode Fayemi ya bayyana cewa mafi yawan gwamnonin Najeriya sun amince su yi allurar rigakafin cutar korona a gaban talabijin domin duk mutane su gani kuma su shaida.
Fayemi ya fadi haka ne bayan ya kammala ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar gwamnati a Abuja ranar Juma’a.
Ya ce shi da sauran gwamnonin kasar nan sun amince da haka domin su tabbatar wa mutane cewa rigakafin korona ba karya bace kuma da gaske ake yi.
” Kada fa a manta cewa mun dauki darasi a yaki da cutar shan-inna da muka yi a shekarun baya inda a dalilin haka yau an wayi gari Najeriya ta rabu da cutar kwata-kwata.
PREMIUM TIMES ta buga labarin cewa shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, mataimakinsa Yemi Osinbajo da manyan jami’an gwamnati za su yi allurar rigakafin cutar korona a talabijin domin duk mutane su gani a kuma shaida.
Shugaban hukumar kula da cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko NPHCDA, Faisal Shuaib ya ce yin haka zai taimaka wajen karfafa guiwar mutane wajen amincewa da yin rigakafin kuma su yadda ayi musu alluran idan aka kammala shigowa da ruwan maganin rigakafin.
Nan da karshen watan Janairu Najeriya za ta karbi maganin rigakafin cutar korona na Pfizer da BioNTech 100,000.
Sai dai ministan kiwon lafiya Olorunnimbe Mamora ya gargaddi mutanen kasar nan da su kara zage damtse wajen kiyaye sharuddan guje wa kamuwa da cutar korona musamman yanzu da babu tabbacin lokacin da kasan za ta samu maganin rigakafin.
Ya ce Najeriya ba za ta samu maganin rigakafin cutar ba a lokacin da ta tsayar ba wato karshe watan Janairu.