KORONA: Mutum 917 suka kamu ranar Lahadi a Najeriya

0

Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 917 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Lahadi.

Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Lahadi sun nuna cewa Legas ta samu karin mutum –214, FCT-222, Kaduna-119, Filato-92, Nasarawa-50, Oyo-41, Adamawa-33, Ondo-32, Abia-28, Ogun-19, Rivers-17, Kano-16, Yobe-14, Edo-8, Anambra-6, Ekiti-5 da Jigawa-1

Yanzu mutum 90,080 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 75,044 sun warke, 1,311 sun rasu.Sannan kuma zuwa yanzu mutum 13,725 ke dauke da cutar a Najeriya.

A ranar Asabar, mutum 576 suka kamu a Najeriya, jihohin Legas, Oyo, Nasarawa, Sokoto da Babban birnin Tarayya, Abuja ne suka fi yawan wadanda suka kamu.

Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 31,321, FCT –12,083, Oyo – 4,035, Edo –2,888, Delta –1,888, Rivers 3,572, Kano –2,324, Ogun–2,552, Kaduna –5,447, Katsina -1,636, Ondo –1,843, Borno –796, Gombe –1,272, Bauchi –1,020, Ebonyi –1,107, Filato – 4,997, Enugu –1,382, Abia – 1,028, Imo –766, Jigawa –406, Kwara –1,414, Bayelsa –519, Nasarawa –898, Osun –1,019, Sokoto –380, Niger – 417, Akwa Ibom – 437, Benue – 532, Adamawa – 424, Anambra – 328, Kebbi – 173, Zamfara –112, Yobe – 201, Ekiti –407, Taraba- 217, Kogi – 5, da Cross Rivers – 169.

Masu tallar maganin gargajiya na cewa, “sai an gwada a kan san na kwarai.” Kamar haka shi ma Shugaban Cocin SCOAN, T.B Joshua, ya yi ikirarin fitar da wani ruwan bagaja da kuma hatimin da ya ce su na warkar da cutar korona da sauran cututtukan da ke damun jama’a.

T.B Joshua dai ya ce wannan ruwan bagaja da hatimi duk wahayin ilhama ce aka yi masa, inda aka umarce shi da ya fitar da ruwan da hatimin ga jama’a.

Ya ce zaman wani dogon lokacin da ya je ya yi a kan tsauni ne aka yi masa wahayin ruwa da hatimi, wadanda a yanzu ya fitar domin jama’a su samu waraka daga cutar korona da sauran cututtuka.

Ita wannan shegiyar cuta wato korona da ku ke ji, ta na zuwa ne a matakai uku. An ga matakin farko, yanzu kuma mun shiga mataki na biyu, wanda shi ne mai tsanani, amma ba dukan kasashen duniya wannan mataki na korona na biyu zai fantsama ba.

Ya ce dalili kenan ubangiji ya ba shi ruwan bagaja da htimi. Ya kara da cewa yanzu abu ya baci, har makwauci da makwauci na tsoron haduwa da juna.

Ya ce hadin ruwan na bagaja da hatimi babu cutar da ba za su iya warkarwa ba.

“Baya ga korona, su na warkar da karayar arziki, raba bawa da gadajjen talauci da kowace irin cuta a duniya.

“Don haka jama’a su zaburo su yi amanna da wannan ruwa da hatimi wanda ubangiji ya ba ni a lokacin da na yi zaman wurdin tsawon lokaci a kan tsauni.

“ Haka ruwan ya na maganin mugun bakin da aka yi wa wani aka ce ba zai taba yin arziki ba. Shi ma wanda jarin sa ya karye a kasuwa da wanda ya kasa samun daukaka a wurin aiki, to ya sha ruwan bagaja kuma ya daura hatimi zai warke.”

Har yanzu dai babu takamaimen maganin korona na asibiti ko na gargajiya. Amma ana ci gaba da gwaje-gwaren alluran rigakafin ta.

Share.

game da Author