Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 864 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Alhamis.
Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Alhamis sun nuna sun nuna cewa babban birin tarayya ta samu karin mutum – FCT-129, Anambra-87, Rivers-82, Benue-80, Oyo-76, Filato-61, Kaduna-54, Delta-51, Nasarawa-38, Kwara-36, Edo-32, Katsina-26, Kano-24, Taraba-18, Ogun-14, Sokoto-11, Gombe-10, Jigawa-7, Akwa Ibom-6, Cross River-6, Zamfara-5, Bauchi-5, Osun-4 da Ekiti-2
Yanzu mutum 127,024 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 100,858 sun warke, 1,547 sun rasu. Sannan zuwa yanzu mutum 24,619 ke dauke da cutar a Najeriya.
Ranar Laraba, mutum 1,861 suka kamu a Najeriya, jihohin Filato, Oyo, Nasarawa, Rivers, Kaduna da Babban birnin Tarayya, Abuja ne suka fi yawan wadanda suka kamu.
Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum –46,935, FCT–16,470, Filato –7,801, Kaduna–7,512, Oyo–5,308, Rivers–5,175 Edo–3,721, Ogun–3,277, Kano–2,913, Delta–2,300, Ondo–2,222, Katsina–1,838, Enugu–1,738, Kwara–1,923, Gombe–1,591, Nasarawa–1,758, Ebonyi–1,393, Osun–1,474, Abia–1,220, Bauchi–1,141, Borno-900, Imo–1,046, Sokoto – 718, Benue- 239, Akwa Ibom–789, Bayelsa 661, Niger–688, Adamawa–631, Anambra–807, Ekiti–534, Jigawa 457, Taraba 367, Kebbi 267, Yobe-221, Cross River–195, Zamfara 199, Kogi–5.
Fitaccen Attajiri kuma gogan mai yi wa kasashe hidima ta hanyar basu tallafi musamman a fannin kiwon Lafiya, Bill Gates ya yi kira ga mahukunta a Najeriya da su mai da hankali wajen inganta fannin kiwon lafiyar Kasar maimakon kokawar siyan rigakafin Korona.
Ya ce kamata ya yi Najeriya ta yi amfani da kudadenta wajen inganta cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko domin talakawanta musamman yara kanana su samu kiwon lafiya nagari ba narka kudi ba wajen mallakar ruwan rigakafin Korona ba.
Gate ya bayyana haka a matsayin shawarar sa ga mahukunta a kasar ganin yadda gwamnatin ta ware naira biliyan 400 domin siyo rigakafin Korona domin ‘yan kasar wanda ba ma duka za su samu da wannan kudi da gwamnati ta ware ba.
Najeriya za ta siya kowane kwalban maganin rigakafin akan dala $8.