Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 576 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Asabar.
Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Asabar sun nuna cewa Legas ta samu karin mutum –277, FCT-90, Oyo-51, Nasarawa-49, Sokoto-23, Anambra-14, Bauchi-11, Imo-11, Kano-11, Edo-10, Plateau-10, Ogun-9, Osun-5, Jigawa-3, Rivers-2.
Yanzu mutum 89,163 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 74,789 sun warke, 1,302 sun rasu.Sannan kuma zuwa yanzu mutum 13,072 ke dauke da cutar a Najeriya.
A ranar Juma’a, mutum 1,074 suka kamu a Najeriya, jihohin Legas, Kaduna, Rivers, Gombe, Kano da Babban birnin Tarayya, Abuja ne suka fi yawan wadanda suka kamu.
Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 31,107, FCT –11,861, Oyo – 3,994, Edo –2,880, Delta –1,888, Rivers 3,555, Kano –2,308, Ogun–2,533, Kaduna –5,328, Katsina -1,636, Ondo –1,811, Borno –796, Gombe –1,272, Bauchi –1,020, Ebonyi –1,107, Filato – 4,905, Enugu –1,382, Abia – 1,000, Imo –766, Jigawa –406, Kwara –1,414, Bayelsa –519, Nasarawa –848, Osun –1,019, Sokoto –380, Niger – 417, Akwa Ibom – 437, Benue – 532, Adamawa – 391, Anambra – 322, Kebbi – 173, Zamfara –112, Yobe – 187, Ekiti –410, Taraba- 217, Kogi – 5, da Cross Rivers – 169.
Jami’an kula da lafiya, sun bayyana cewa a matsayin su na wadanda ke sahun farkon saida rai domin su ceto rayukan wasu, su na bukatar karin kudaden alawus.
Sun ce naira 5,000 kacal da ake ba kowanen su a matsayin alawus din saida rayukan su domin su ceto rayukan wasu, wato ‘hazard allowances’ sun yi kadan matuka.
Da ya ke magana a taron nesa-nesa, Shugaban Kungiyar Likitoci ta Najeriya (NMA), Innocent Ujah, ya bayyana cewa dukkan jami’an kula da lafiya naira 5,000 kacal ake ba kowanen su a matsayin kudaden alawus din saida rayukansu.
“Duk da irin saida ran da su ke yi a cikin wannan mawuyacin yanayi, wanda ake kara samun yawaitar mace-mace, amma har yau alawus din naira 5,000 ce kadai ake bai wa kowanen su.”
Mene Ne Alawus Din A Saida Rai Na Jami’an Lafiya?:
Alawus din saida rai don a ceci ran marasa lafiya dai wasu kudade ne da aka dora wa jami’an kula da lafiya, saboda gudanar da ayyuka masu hatsarin gaske da su ke yi, tun bayan bullar cutar korona a Najeriya.
Su dai jami’an kula da lafiya, su ne a sahun farko na masu jefa kan su cikin hatsari wajen mu’amala da masu dauke da ciwon korona.
Duk da cewa an sha gargadin su da su rika amfani da cikakkun kayan kariyar jiki daga cutar korona daga wurin wadanda su ka kamu da cutar, da yawan wadannan jami’ai na kiwon lafiya ba su da sukunin mallakar kayan kariyar, wato PPE, ko ‘Personal Protection Equipment’ a Turance.
A zuwa karshen watan Yuli dai sama da jami’an lafiya 10,000 ne su ka kamu da cutar korona a Najeriya, wadanda akasarin su duk daga wurin wadanda su ka kamu da cutar su kuma su ka dauka.
An sha yi masu alkawari, amma ba a cikawa.
Cikin makonni biyu da su ka gabata, an tabbatar da cewa cutar korona ta kashe likitocin Najeriya har su 20, lamarin da Shugaba Muhammadu Buhari da kan say a ce abin bakin ciki ne, a cikin takardar ta’aziyyar da ya aika wa Kungiyar Likitoci ta Najeriya.
Cikin watan Afrilu dai gwamnatin Buhari ta yi masu alkawarin ba su kudaden alawus da karin kudade har kashi 50 bisa 100 na gundarin albashin su, amma har yau shiru ka ke ji.
Discussion about this post