Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 1114 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Juma’a.
Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Juma’a sun nuna sun nuna cewa babban birin tarayya ta samu karin mutum – 408, FCT-95, Filato-90, Ondo-66, Kaduna-63, Oyo-56, Borno-46, Imo-42, Edo-41, Ogun-37, Rivers-31, Ekiti-25, Yobe-20, Kano-18, Akwa Ibom-18, Delta-15, Osun-15, Kwara-11, Bayelsa-6, Nasarawa-6, Zamfara-4 da Bauchi-1.
Yanzu mutum 128,674 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 102,780 sun warke, 1,577 sun rasu. Sannan zuwa yanzu mutum 24,317 ke dauke da cutar a Najeriya.
Ranar Alhamis, mutum 864 suka kamu a Najeriya, jihohin Filato, Oyo, Rivers, Benue, Anambra, da Babban birnin Tarayya, Abuja ne suka fi yawan wadanda suka kamu.
Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum –47,879, FCT–16,565, Filato –7,891, Kaduna–7,575, Oyo–5,364, Rivers–5,206, Edo–3,762, Ogun–3,314, Kano–2,931, Delta–2,315, Ondo–2,288, Katsina–1,838, Enugu–1,738, Kwara–1,934, Gombe–1,591, Nasarawa–1,764, Ebonyi–1,393, Osun–1,489, Abia–1,220, Bauchi–1,142, Borno-946, Imo–1,088, Sokoto – 718, Benue- 829, Akwa Ibom–807, Bayelsa 667, Niger–688, Adamawa–631, Anambra–807, Ekiti–559, Jigawa 457, Taraba 367, Kebbi 267, Yobe-241, Cross River–195, Zamfara 203, Kogi–5.
Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar III ya yi kira ga gwamnatin da ta fadada kamfen din wayar da kan mutane game da allurar rigakafin cutar korona da za a shigo da su a watan Faburairu.
Sa’ad ya ce yin haka zai taimaka wajen kawar da rudanin da rashin yarda a tsakanin mutane wanda shine yanzu ya karade gari.
Ya fadi haka a taron wayar da kan malamai da limaman kasar nan game da maganin rigakafin Korona da hukumar kula da cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko na ƙasa NPHCDA ta shirya.
Discussion about this post