Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 1,633 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Asabar.
Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Asabar sun nuna sun nuna cewa Legas ta samu karin mutum –498, Filato-214, FCT-176, Rivers-99, Kaduna-98, Edo-87, Anambra-86, Akwa Ibom-50, Osun-47, Kano-40, Oyo-40, Kwara-39, Ebonyi-28, Niger-28, Taraba-28, Ogun-27, Ondo-21, Ekiti-12, Katsina-7, Borno-6 da Delta-2
Yanzu mutum 120,602 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 95,901 sun warke, 1,502 sun rasu. Sannan zuwa yanzu mutum 23,933 ke dauke da cutar a Najeriya.
A ranar Juma’a, mutum 1483 suka kamu a Najeriya, jihohin Filato, Kaduna, Oyo, Nasarawa da Babban birnin Tarayya, Abuja ne suka fi yawan wadanda suka kamu.
Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum –44,580, FCT–15,682, Filato –7,465, Kaduna–7,274, Oyo–4,996, Rivers–4,844, Edo–3,548, Ogun–3,133, Kano–2,770, Delta–2,223, Ondo–2,188, Katsina–1,730, Enugu–1,644, Kwara–1,793, Gombe–1,567, Nasarawa–1,490, Ebonyi–1,330, Osun–1,395, Abia–1,162, Bauchi–1,120, Borno–880, Imo–917, Sokoto – 689, Benue 694, Akwa Ibom–775, Bayelsa 655, Niger–617, Adamawa–608, Anambra–720, Ekiti–507, Jigawa 441, Taraba 324, Kebbi 267, Yobe-211, Cross River–179, Zamfara 179, Kogi–5.
Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ya bayyanawa manema Labaria a garin Cewa gwamnati za ta kafa kungiyar duba garin Korona a jihar Kano.
Gwamna Ganduje ya ce gwamnati ta yi haka ne domin a tilasta wa mutane bi da kiyaye dokokin korona a fadin jihar.
” Dole mu maida hankali matuka wajen kawo karshen yaduwar cutar Korona a jihar Kano. Ba za mu sa ido mu bari ta ci gaba da fantsama a tsakanin mutanen mu ba.
Ganduje ya ce za a kafa wannan kungiya ta hadin gambiza ce, wanda zai hada da jami’an ‘yan sanda, Sibul Difens da wasu da za a dauka domin tabbatar an yi nasara a wannan aiki.
A karshe Ganduje godewa masu makarantu masu zaman kansu kan yadda suke kokarin taimakawa gwamnati wajen kiyaye dokar Korona.