KORONA: Mutum 15 sun rasu, 1,303 suka kamu ranar Talata a Najeriya

0

Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 1,303 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Talata.

Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Talata sun nuna sun nuna cewa Legas ta samu karin mutum –478, FCT-211, Nasarawa-83, Rivers-72, Kwara-42, Edo-36, Ondo-34, Benue-32, Kaduna-32, Katsina-26, Filato-26, Kano-25, Taraba-25, Osun-22, Delta-21, Oyo-21, Niger-19, Sokoto-18, Ebonyi-17, Ekiti-14, Gombe-13, Ogun-12, Bauchi-11, Zamfara-8, Borno-4 da Jigawa-1.

Yanzu mutum 124,299 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 99,276 sun warke, 1,522 sun rasu. Sannan zuwa yanzu mutum 23,501 ke dauke da cutar a Najeriya.

Ranar Litini, mutum 1,430 suka kamu a Najeriya, jihohin Filato, Oyo, Nasarawa, Katsina da Babban birnin Tarayya, Abuja ne suka fi yawan wadanda suka kamu.

Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum –46,162, FCT–16,056, Filato –7,648, Kaduna–7,399, Oyo–5,094, Rivers–4,982, Edo–3,646, Ogun–3,251, Kano–2,862, Delta–2,244, Ondo–2,222, Katsina–1,804, Enugu–1,681, Kwara–1,867, Gombe–1,581, Nasarawa–1,637, Ebonyi–1,374, Osun–1,458, Abia–1,203, Bauchi–1,131, Borno–896, Imo–989, Sokoto – 707, Benue 749, Akwa Ibom–783, Bayelsa 655, Niger–688, Adamawa–608, Anambra–720, Ekiti–532, Jigawa 446, Taraba 349, Kebbi 267, Yobe-221, Cross River–189, Zamfara 193, Kogi–5.

A watan Satumba Kasar Birtaniya ta sanar da bayyanar wata sabuwar samfurin Korona da take mamaye mutanen kasar sannan ana samun karin mutanen kasar da ke ta mutuwa babu kakkautawa da dalilin kamuwa da wannan cuta.

Ita dai wannan nau’in Korona mai suna “lineage B.1.1.7” ta bayyana da tsanani a kasar Birtaniya, yasa dole gwamnatin kasar ta saka sabbin dokoki na dakile yaduwarta da suka hada da dokar shiga da fice da balaguro a fadin kasar.

Sai dai bayan watanni 4 da fadin haka shugaban kwamitin PTF Boss Mustapha ya bayyana cewa an samu bayyanar wannan nau’i na Korona B117 a Najeriya.

Mustapha ya ce masana kimiya sun gano wannan nau’i na cutar ne bayan an dauki lokaci mai tsawo ana gudanar da bincike akan cutar.

“Masana kimiya da kwamitin PTF sun gudanar da bincike akan dalilin da ya sa ake samun karuwa a yaduwar cutar makonnin da suka gabata a kasar nan.

“Sakamakon binciken da masana kimiya suka yi ya nuna cewa akwai burbudin kwayoyin B117 a kasar nan.

Share.

game da Author