Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 1,354 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Talata.
Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Talata sun nuna cewa Legas ta samu karin mutum –712, FCT-145, Filato-117, Kwara-81, Kaduna-54, Sokoto-39, Oyo-38, Rivers-37, Gombe-21, Enugu-20, Akwa Ibom-16, Bauchi-14, Delta-14, Ebonyi-13, Anambra-9, Taraba-8, Edo-8, Kano-3, Osun-2, Ekiti-2 da Ogun-1.
Yanzu mutum 92,705 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 76,396 sun warke, 1,319 sun rasu.Sannan kuma zuwa yanzu mutum 14,990 ke dauke da cutar a Najeriya.
A ranar Litini mutum 1,204 suka kamu a Najeriya, jihohin Legas, Kaduna, Filato, Kano, Rivers da Babban birnin Tarayya, Abuja ne suka fi yawan wadanda suka kamu.
Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 32,687, FCT –12,428, Oyo – 4,086, Edo –2,938, Delta –1,911, Rivers 3,639, Kano –2,367, Ogun–2,564, Kaduna –5,555, Katsina -1,636, Ondo –1,843, Borno –808, Gombe –1,359, Bauchi –1,052, Ebonyi –1,120, Filato – 5,174, Enugu –1,420, Abia – 1,036, Imo –769, Jigawa –407, Kwara –1,495, Bayelsa –545, Nasarawa –923, Osun –1,022, Sokoto –420, Niger – 417, Akwa Ibom – 465, Benue – 537, Adamawa – 424, Anambra – 337, Kebbi – 192, Zamfara –112, Yobe – 201, Ekiti –417, Taraba- 225, Kogi – 5, da Cross Rivers – 169.
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa Najeriya za ta karbi maganin rigakafin cutar korona na Pfizer da BioNTech 100,000 a karshen watan Janairu.
Shugaban hukumar cibiyar kiwon lafiya na matakin farko na ƙasa, NPHCDA Faisal Shuaib ya ce kamfanin COVAX wanda ya dauki nauyin shigo da magungunan zai shigo da kwalaben maganin 100,000 sannan daga baya kamfanin ya kara shigowa da miliyan 42 na maganin a matsayin gudunmawar kamfanonin vaccine alliance da GAVI wa Najeriya.
Ya ce maganin rigakafin guda miliyan 42 din da za a shigo da su zai kunshi ire-iren magungunan rigakafin cutar da hukumomin kula da lafiya na duniya suka amince da su sannan daga ciki zai isa ayi wa akalla kashi 20 bisa 100 na mutum miliyan 200 da ke kasar nan.
Idan ba a manta ba gwamnati ta kafa kwamitin mutum 18 wanda za su tabbatar Najeriya ta samu maganin rigakafin cutar korona da zaran hukumomin lafiya sun amince da shi.
Discussion about this post