Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 1,430 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Litini.
Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Litini sun nuna sun nuna cewa Legas ta samu karin mutum –744, Filato-100, Oyo-77, FCT-75, Nasarawa-74, Katsina-48, Edo-42, Kano-41, Enugu-37, Rivers-34, Ogun-33, Kwara-32, Niger-28, Ebonyi-27, Kaduna-26, Borno-12, Yobe-10
Ekiti-5, Gombe-1.
Yanzu mutum 112,996 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 98,359 sun warke, 1,507 sun rasu. Sannan zuwa yanzu mutum 23,568 ke dauke da cutar a Najeriya.
Ranar Lahadi, mutum 964 suka kamu a Najeriya, jihohin Filato, Kaduna, Ogun, Imo da Babban birnin Tarayya, Abuja ne suka fi yawan wadanda suka kamu.
Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum –45,684, FCT–15,845, Filato –7,622, Kaduna–7,367, Oyo–5,073, Rivers–4,910, Edo–3,610, Ogun–3,239, Kano–2,837, Delta–2,223, Ondo–2,188, Katsina–1,778, Enugu–1,681, Kwara–1,825, Gombe–1,568, Nasarawa–1,554, Ebonyi–1,357, Osun–1,436, Abia–1,203, Bauchi–1,120, Borno–892, Imo–989, Sokoto – 689, Benue 717, Akwa Ibom–783, Bayelsa 655, Niger–669, Adamawa–608, Anambra–720, Ekiti–518, Jigawa 445, Taraba 324, Kebbi 267, Yobe-221, Cross River–189, Zamfara 185, Kogi–5.
Wani babban likitan kwakwalwa Philip Njemanze ya gargadi gwamnatin Najeriya ta kula matuka sannan ta yi karatun ta natsu kan kokarin siyo maganin rigakafin Korona da ta ke kokarin domin ‘yan kasar nan.
” Yakamata gwamnatin Najeriya ta yi watsi da shirinta na sayen alluran rigakafi daga kamfanonin hada magunguna da kuma mai da hankali kan ba da maganin na Ivermectin wa ‘yan Najeriya,”
Da yake jawabi a wani taron tattaunawa mai taken ‘Bayani don kwararrun kiwon lafiya da kuma kafofin watsa labarai a kan allurar rigakafin Pfitzer / BioNTech COVID-19, Njemanze ya ce akwai bukatar gwamnati ta dauki matakan shawo kan cutar ta hanyar ba da magungunan da za su taimaka wa jiki yakar cutar da rage kwayar cuta.
Ya kara da cewa maimakon kashe kudade kan allurar rigakafin, ya kamata Gwamnatin Tarayya ta ba Ivermectin fifiko wajen magance cutar a musamman ‘yan kasar nan.
Ivermectin shine ya fi dacewa mu maida hankali wajen amfani da shi tukunna tunda farko.
Abinda ya kamata a kula dashi shine ita Koronan ma tana rikidewa ne fa lokaci lokaci, idan aka bada rigakafin Pfitzer cutar ta rikide kwai fa babban kalubale kenan fa, za afada cikin rudani kenan.