Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 1024 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Lahadi.
Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Lahadi sun nuna cewa Legas ta samu karin mutum –653, Filato-63, Benue-48, Zamfara-45, FCT-42, Rivers-27
Ondo-26, Adamawa-26, Kaduna-22, Edo-18, Ogun-16, Imo-12, Kano-9, Yobe-6
Ekiti-5, Jigawa-4 da Osun-2.
Yanzu mutum 100,087 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 80,030 sun warke, 1,358 sun rasu. Sannan zuwa yanzu mutum 18,699 ke dauke da cutar a Najeriya.
A ranar Asabar, mutum 1,544 suka kamu a Najeriya, jihohin Legas, Filato, Oyo, Nasarawa, Rivers da Babban birnin Tarayya, Abuja ne suka fi yawan wadanda suka kamu.
Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 36,101, FCT –13,448, Oyo – 4,323, Edo –3,078, Delta –1,982, Rivers 3,913, Kano –2,444, Ogun–2,684, Kaduna –5,801, Katsina -1,687, Ondo –1,944, Borno –830, Gombe –1,440, Bauchi –1,082, Ebonyi –1,147, Filato – 5,774, Enugu –1,455, Abia – 1,086, Imo –801, Jigawa –419, Kwara –1,495, Bayelsa –569, Nasarawa – 1,091, Osun –1,065 , Sokoto –529, Niger – 477, Akwa Ibom – 512, Benue – 601, Adamawa – 497, Anambra – 386, Kebbi –223, Zamfara –157, Yobe – 207, Ekiti –439, Taraba- 226, Kogi – 5, da Cross Rivers – 169.
Karamin ministan kiwon lafiya Olorunnimbe Mamora ya zayyano wasu dalilai da ya sa Najeriya ke samun karuwa a yawan mutanen dake mutuwa sanadiyyar kamuwa da Korona.
Mamora ya ce hakan na faruwa ne a dalilin rashin gaggauta zuwa asibiti da wadanda suka kamu ba su yi.
Ya ce kamata ya yi a rika gaggawar zuwa asibiti da zaran an ga alamun cutar a jiki ba kawai a zauna a gida ana ‘yan dabaru ba.
Bayan haka Mamora ya ce gwamnati na kokarin ganin ta wadata wuraren da ake kula da wadanda suka kamu da korana na’uran samar da iska domin bunkasa aiyukkan inganta kiwon lafiyar marasa lafiya.
Daga nan wasu kwararrun ma’aikatan lafiya sun ce rashin kiyaye sharuddan guje wa kamuwa da cutar da mutane ke yi musamman a jihohi Legas, Kaduna, Filato da babban birnin tarayya Abuja na cikin dalilan da ya sa cutar ke yawan kisan mutane a kasar nan.
Kwararrun sun yi gargadin cewa yaduwar cutar zai karu fiye da yadda ake tsammani idan mutane suka ci gaba da karya sharuddan
Discussion about this post