KORONA: Kwana biyu a jere mutum 1 ke kamuwa a jihar Jigawa, mutum 1,565 suka kamu ranar Alhamis

0

Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 1,565 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Alhamis.

Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Alhamis sun nuna cewa Legas ta samu karin mutum –807, FCT-236, Kaduna-79, Oyo-57, Filato-47, Rivers-37, Katsina-35, Edo-30, Sokoto-30, Delta-26, Kebbi-23, Ondo-20, Enugu-18, Abia-17
Ogun-17, Benue-16, Bayelsa-15, Bauchi-14, Niger-13, Kano-10, Borno-6, Imo-5, Ekiti-4, Osun-2 da Jigawa-1

Yanzu mutum 95,934 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 77,982 sun warke, 1,330 sun rasu. Sannan zuwa yanzu mutum 16,622 ke dauke da cutar a Najeriya.

A ranar Laraba mutum 1664 suka kamu a Najeriya, jihohin Legas, Kaduna, Filato, Rivers, Adamawa da Babban birnin Tarayya, Abuja ne suka fi yawan wadanda suka kamu.

Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 34,136, FCT –13,071, Oyo – 4,157, Edo –2,996, Delta –1,944, Rivers 3,738, Kano –2,389, Ogun–2,605, Kaduna –5,717, Katsina -1,671, Ondo –1,863, Borno –823, Gombe –1,359, Bauchi –1,071, Ebonyi –1,120, Filato – 5,381, Enugu –1,445, Abia – 1,082, Imo –789, Jigawa –410, Kwara –1,495, Bayelsa –560, Nasarawa –961, Osun –1,036, Sokoto –455, Niger – 454, Akwa Ibom – 465, Benue – 553, Adamawa – 471, Anambra – 364, Kebbi –215, Zamfara –112, Yobe – 201, Ekiti –426, Taraba- 225, Kogi – 5, da Cross Rivers – 169.

Bayan haka Shugaban kwamitin Shugaban Kasa na PTF Boss Mustapha ya bayyana cewa ‘yan bautan ƙasa 731 sun kamu da cutar Korona a Najeriya.

Ya ce an gano haka ne bayan gwajin cutar da aka yi wa ‘yan bautan ƙasar na rukuni na B su 35,419 a duka sansanonin dake fadin kasar nan.

Idan ba a manta ba a kwanakin baya gwamnati ta yi wa ‘yan rukunin farko wato A gwajin cutar inda daga ciki aka samu masu bautar kasa 108 sun kamu.

Bayan haka watanni biyu da suka gabata PREMIUMTIMES HAUSA ta buga labarin yadda ‘yan bautan ƙasa 138 suka kamu da korona a fadin kasar nan.

Share.

game da Author