Mutum 1,301 suka kamu ranar Talata, Abuja, Filato da Kaduna ke kan gaba wajen yawan mutanen da ta diba
Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 1,301 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Talata.
Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Talata sun nuna cewa Legas ta samu karin mutum –551, FCT-209, Oyo-83, Filato-65, Kaduna-64, Enugu-61, Rivers-44, Ondo-39, Benue-37, Akwa Ibom-31, Kano-19, Delta-18, Gombe-18, Ogun-16, Edo-15, Kebbi-10, Ebonyi-9, Jigawa-4, Osun-3, Zamfara-3, Borno-1 da Nasarawa-1.
Yanzu mutum 113,305 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 91,200 sun warke, 1,464 sun rasu. Sannan zuwa yanzu mutum 20,641 ke dauke da cutar a Najeriya.
A ranar Litini, mutum 1,617 suka kamu a Najeriya, jihohin Legas, Filato, Kaduna, Kwara, Edo da Babban birnin Tarayya, Abuja ne suka fi yawan wadanda suka kamu.
Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum –41,951, FCT–14,909, Filato –6,896, Kaduna–6,389, Oyo–4,778, Rivers–4,473, Edo–3,335, Ogun–2,928, Kano–2,636, Delta–2,140, Ondo–2,109, Katsina–1,723, Enugu–1,644, Kwara–1,697, Gombe–1,518, Nasarawa–1,336, Ebonyi–1,284, Osun–1,263, Abia–1,134, Bauchi–1,107, Borno–868, Imo–857, Sokoto – 677, Benue 694, Akwa Ibom–698, Bayelsa 619, Niger–547, Adamawa–573, Anambra–515, Ekiti–473, Jigawa 429, Taraba 294, Kebbi 261, Yobe-211, Cross River–169, Zamfara 165, Kogi–5.
Shugaban hukumar kula cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko na ƙasa NPHCDA Faisal Shu’aib ya karyata labaran da ake yadawa wai rigakafin Korona karya ce cuta ce ake neman a dirka wa mutanen Najeriya.
Faisal ya bayyana cewa babu wani ciri na makirci da aka yi game da maganin rigakafin Korona kamar yadda wasu ke fadi.
” Maganin rigakafin Korona magani ne da aka hada shi ta hanyar bin dokoki da sharuddan hada magunguna da kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO ta tsara.
” Babu wani guba da aka saka a cikin ruwan maganin da zai illatar da mutane a kasar nan.”
Faisal ya ce gwamnati za ta ci gaba da wayar wa mutane kai game da muhimmancin kowa da kowa ya yi alluran idan aka samar da su.
Idan ba a manta ba PREMIUMTIMES ta buga labarin yadda Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da mataimakinsa Yemi Osinbajo suka amince su yi allurar rigakafin cutar a talabijin domin duk mutane su shaida.
Ita ma kungiyar gwamnonin Najeriya sun shaida cewa za su yi allurar rigakafin korona da zaran an shigo da maganin kasar nan.
Kungiyar ta ce yin haka zai taimaka wajen karfafa gwiwar mutane su yi allurar.
Bayan haka Faisal ya ce gwamnati ta dauki duk wani mataki da zai taimaka wajen ganin an ci nasaran yi wa mutane rigakafin.
Ya ce abin da ya hada da gina wurin adana ruwan maganin rigakafin, na’uran yin allurar da dai sauran su na cikin shirye-shiryen da gwamnati ta yi.
A makon da ya gabata ne gwamnatin tarayya ta sanar cewa za ta karbi kwalaban maganin rigakafin guda 100,000 a karshen watan Janairu.
Gwamnati ta kuma ce kamfanin hada magunguna GAVI za ta yi gudunmawar kwalaban maganin miliyan 42 wa Najeriya.
Bisa ga lissafin gwamnati maganin zai iya yi wa kashi 20 daga cikin mutum miliyan 200 dake zama a kasar nan ne kawai.