Gwamnatin jihar Kano ta umarci duka ma’aikatan gwamnatin jihar su zauna a gida zuwa wani lokaci saboda fantsamar Korona da ya darkako jihar.
Bayan ma’aikata da aka umarta su zauna a gida, gwamnati ta rufe duka gidajen kallo da taron bukukuwa a fadin jihar.
A tsakanin makonni hudu, mutane 10 suka rasu a jihar a dalilin Korona. Yanzu wadanda suka mutu a Kano saboda Kotona sun kai 70.
Kwamishinan Yada labarai na jihar, Garba Muhammda ya ce gwamnati ta dauki wannan mataki ne ganin yadda annobar take cigaba da fantsama a jihar sannnan kuma da mutuwa da mitane keyi adalilin wannan cuta.
Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 1,617 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Litini.
Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Litini sun nuna cewa Legas ta samu karin mutum –776, Kaduna-147, Kwara-131, FCT-102, Filato-78, Edo-59, Ogun-53, Osun-45, Rivers-37, Taraba-36, Nasarawa-34, Adamawa-33, Kano-26, Delta-20, Ebonyi-16, Bayelsa-11, Gombe-11 da Borno-2
Yanzu mutum 112,004 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 89,939 sun warke, 1,449 sun rasu. Sannan zuwa yanzu mutum 20,616 ke dauke da cutar a Najeriya.
A ranar Lahadi, mutum 1444 suka kamu a Najeriya, jihohin Legas, Filato, Kaduna, Ebonyi, Akwa Ibom da Babban birnin Tarayya, Abuja ne suka fi yawan wadanda suka kamu.
Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum –41,400, FCT–14,700, Filato –6,831, Kaduna–6,325, Oyo–4,695, Rivers–4,429, Edo–3,320, Ogun–2,912, Kano–2,617, Delta–2,122, Ondo–2,070, Katsina–1,723, Enugu–1,583, Kwara–1,697, Gombe–1,500, Nasarawa–1,335, Ebonyi–1,275, Osun–1,260, Abia–1,134, Bauchi–1,107, Borno–867, Imo–857, Sokoto – 677, Benue 657, Akwa Ibom–667, Bayelsa 608, Niger–547, Adamawa–573, Anambra–515, Ekiti–473, Jigawa 425, Taraba 294, Kebbi 251, Yobe-211, Cross River–169, Zamfara 162, Kogi–5.
Cibiyar Binciken Lakanin Hada Magunguna ta Kasa, NIPRD, ta bayyana cewa ta gano wasu sinadarai da lakanin da idan an harhada za a iya samar da maganin warkar da cutar Korona.
Discussion about this post