Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 1398 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Laraba.
Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Laraba sun nuna cewa Legas ta samu karin mutum –542, FCT-131, Oyo-120, Rivers-113, Filato-111, Kaduna-71, Kwara-71, Akwa Ibom-34, Sokoto-31, Benue-28, Ogun-27, Kano-26, Kebbi-17, Osun-12, Nasarawa-11, Delta-10, Gombe-10, Bayelsa-9, Borno-9
Edo-8, Ekiti-3, Jigawa-2 da Katsina-2.
Yanzu mutum 103,999 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 82,555 sun warke, 1,382 sun rasu.Sannan zuwa yanzu mutum 20,062 ke dauke da cutar a Najeriya.
A ranar Talata, mutum 1270 suka kamu a Najeriya, jihohin Legas, Filato, Oyo, Rivers, Enugu da Babban birnin Tarayya, Abuja ne suka fi yawan wadanda suka kamu.
Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 37,852, FCT –13,938, Oyo – 4,546, Edo –3,143, Delta –2,031, Rivers 4,124, Kano –2,491, Ogun–2,727, Kaduna –5,888, Katsina -1,692, Ondo –2,006, Borno –844, Gombe –1,467, Bauchi –1,100, Ebonyi –1,159, Filato – 6,073, Enugu –1,506, Abia – 1,095, Imo –806, Jigawa –421, Kwara –1,566, Bayelsa –586, Nasarawa –1,153, Osun –1,110, Sokoto –590, Niger – 508, Akwa Ibom – 553, Benue – 629, Adamawa – 497, Anambra –433, Kebbi –240, Zamfara –159, Yobe – 207, Ekiti –446, Taraba- 239, Kogi – 5, da Cross Rivers – 169.
Sakamakon gwajin cutar Korona da aka yi a kasar Amurka Kuma aka fitar ranar Alhamis ya nuna cewa akalla mutum 4,000 sun rasu cikin awa 24 a kasar.
Wannan shine karo na farko da kasar ta samu yawan mutanen da suka rasu a ra a daya a wannan lokaci.
Bisa ga rahotan jaridar ‘Washington Post mutum 3900 ne suka mutu a dalilin kamuwa da cutar a kasar.
Masana kimiya da masana magungunan sun hada maganin rigakafin korona kuma kasar Amurka na daga cikin kasashen da suka fara amfani da su sai dai duk da haka mutane sai kara mutuwa suke a dalilin cutar.
Sakamakon jami’ar John Hopkins ya nuna cewa mutum miliyan 21.5 ne suka kamu da cutar a kasar zuwa yanzu. Daga ciki mutum 364,500 sun mutu