Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 964 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Lahadi.
Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Lahadi sun nuna sun nuna cewa Legas ta samu karin mutum – 360, FCT-88, Ogun-73, Imo-72, Kaduna-67, Filato-57, Abia-41, Osun-41, Rivers-32, Kano-26, Niger-24, Benue-23, Edo-20, Cross River-20, Akwa Ibom-8, Nasarawa-6, Zamfara-6, Ekiti-6 da Jigawa-4.
Yanzu mutum 121,566 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 97,228 sun warke, 1,504 sun rasu. Sannan zuwa yanzu mutum 23,568 ke dauke da cutar a Najeriya.
A ranar Asabar, mutum 1,633 suka kamu a Najeriya, jihohin Filato, Kaduna, Rivers,Edo da Babban birnin Tarayya, Abuja ne suka fi yawan wadanda suka kamu.
Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum –44,940, FCT–15,770, Filato –7,522, Kaduna–7,341, Oyo–4,996, Rivers–4,844, Edo–3,548, Ogun–3,206, Kano–2,796, Delta–2,223, Ondo–2,188, Katsina–1,730, Enugu–1,644, Kwara–1,793, Gombe–1,567, Nasarawa–1,496, Ebonyi–1,330, Osun–1,436, Abia–1,203, Bauchi–1,120, Borno–880, Imo–989, Sokoto – 689, Benue 717, Akwa Ibom–783, Bayelsa 655, Niger–641, Adamawa–608, Anambra–720, Ekiti–513, Jigawa 445, Taraba 324, Kebbi 267, Yobe-211, Cross River–189, Zamfara 185, Kogi–5.
A lokacin da cutar korona ke ci gaba da yaduwa a kasar nan sakamakon wani bincike da aka yi ya nuna cewa kashi 17% na tababan anya akwai cutar a Najeriya kuwa.
Sakamakon binciken ya nuna cewa kashi 68.8 na mutanen kasar nan ne kacal suka yadda akwai cutar korona.
Kashi 14.4 bisa 100 kuma suna shakkun ko akwai cutar ko kuma kawai kirkira kawai ake yi, sannan kashi 16.7 basu yarda kwata-kwata wai akwai wata cuta Korona ba, suna ganin duk buge ne.
Kashi 50% na mutanen jihohin Ekiti, Enugu, Kogi, Nasarawa da Sokoto sun yadda cewa lallai akwai Korona a kasar nan.
Kamfanin SBM Intel ne ya gudanar da wannan bincike a jihohi 36 da Abuja.
Binciken ya zakulo ra’ayoyin mutane masu shekaru 18 zuwa 55 game da cutar, matakan dakile yaduwar cutar sannan da rigakafin cutar da ake siyarwa yanzu.
Sakamakon binciken
Mutane a jihohi 23 sun ce a gaskiya ba a kiyaye bin dokokin Korona a kasar nan.
Su kuwa mutanen jihohin Bauchi, Delta da Osun sun ce jama’a na kiyaye bin dokokin gujewa kamuwa da cutar.
39.9% na mutanen Najeriya sun ce za suyi rigakafin cutar idan maganin ya iso Najeriya, kashi 35.9 sun ce ba za su yi rigakafin ba.
Dalilin da ya sa mutane basu yarda da Korona ba
Da yake ba a samun mutane da yawa dake mutuwa saboda Korona ya sa mutane basu yarda akwai cutar ba.
Wasu na cewa wai maganin rigakafin da za a shigo da su guba ne don a kashe mutanen Najeriya.
Kashi 63.3 sun ce koda cutar ta ci gaba da yaduwa kada a saka dokar zaman gida dole.
Amma mutanen dake jihohin Abia da Gombe sun ce gwamnati ta saka dokar zaman gida dole idan har cutar ta ci gaba da yaduwa a kasar nan.