Shugaban hukumar kula da cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko NPHCDA Faisal Shu’aib ya bada Karin haske kan dalilan da ya sa Najeriya ba ta hada maganin rigakafin cututtuka ba a kasar nan.
Faisal ya ce hada maganin rigakafi aiki ne ja dake da wahalar gaske kuma dake bukatar a ware masa makudan kudade na tsawon wani lokaci.
Ya ce idan ba a manta ba bayan Najeriya ta samu ‘yancin kanta kasan ta fara hada maganin rigakafin cututtuka Wanda cutar shawara ke daya daga cikinsu kuma har ake saida wa kasashen waje kamar su Kamaru da wasu kasashen Afrika.
Kamfanin dake Yaba a jihar Legas ya yi aiki daga 1940 zuwa 1991 kafin ya gurgunce.
Pfizer da bioNtech, Moderna da Oxford-AstraZeneca na daga cikin maganin rigakafin da aka amince da su a yanzu sannan kasashen duniya da dama sun yi na ta siyan maganin a yanzu domin yi wa mutanen kasashen su.
Zuwa karshen watan Janairu Najeriya na da ran samun maganin rigakafi 1000 sannan daga baya ta samu wasu guda miliyan 42.
Fara hada maganin rigakafi a Najeriya
A shekaran 2017 tsohon ministan kiwon lafiya Isaac Adewole yace Najeriya ta hada gwiwa da Kamfanin hada magunguna ‘May and Baker’ domin ganin an fara hada maganin rigakafi a kasar nan.
A lokacin Adewale ya ce gwamnati ta kammala shiri tsaf domin ganin haka ya faru amma har yanzu shuru kake ji.
Duk da haka Faisal ya ce gwamnati ta dauki matakai da za su taimaka wajen ganin Najeriya ta fara hada maganin rigakafi.
Discussion about this post