Gwamna Yahaya Bello na Jihar Kogi, wanda ya rika zabga karairayin cewa babu cutar korona a jihar Kogi, yanzu kuma ya bijiro da sabon kamfen, na tinzira jama’a kada su yarda a dankara masu allurar rigakafin cutar korona.
Bello ya fara wannan kamfen a daidai lokacin da duniya baki daya ta maida hankali wajen kirkirowa, samarwa, saye da mallakar rigakafin korona, shi kuma ya maida hankali wajen karyata cutar tare da hana mutane yarda a yi masu rigakafin ta.
Wannan lamari ya za daidai lokacin da gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa ta na zaman jiran kwalaben allurar rigakafin korona daga kamfanin Pfizer da BioNTech nan da karshen watan Janairu.
Sai dai kuma masana harkokin lafiya da kungiyoyin da su ka jibinci lafiya da magunguna na duniya sun shaida wa PREMIUM TIMES cewa, “ba fa zai taba yiwuwa Najeriya ta samu allurar rigakafin korona nan da karshen Janairu ba.’’
Jami’an gwamnati a Fadar Shugaban Kasa sun bayyana cewa Shugaba Muhammadu Buhari da Mataimakin sa Yemi Osinbajo ne za a fara yi wa allurar rigakafin korona a kasar nan.
Sun ce kuma kai tsaye za a nuno su a lokacin da ake yi masu allurar a talbijin kowa ya gani.
Gwamna Kayode Fayemi na Jihar Ekiti, ya gana da Shugaba Buhari, inda bayan ganawar da suka yi ya shaida wa manema labarai cewa su ma gwamnoni a fili za a yi masu allurar kai-tsaye za a nuno a gidajen talbijin.
“Kada fa ku manta, mu na da sani da fahimta a kan batun rigakafin nan. Mun yi kokari mun dakile cutar foliyo ta hanyar rigakafi.” Haka Fayemi ya ce, wanda shi ne Shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya.
Duk Wanda Korona Ba Ta Kashe Ba, To Allurar Rigakafin Korona Za Ta Kashe Shi -Yahaya Bello:
An nuno Gwamna Yahaya Bello na Jihar Kogi a cikin wani bidiyo ya na ingiza mutane kada su sake su yarda a yi masu allurar rigakafin korona.
Bidiyon dai tun a ranar Lahadi aka fara watsa shi a soshiyal miiya, musamman a shafukan Facebook.
“..Su na so su yi amfani da rigakafin korona su kashe ku, su kashe mu. Allah ya kiyaye! Wa zai yarda a yi masa allurar korona!” Inji Yahaya Bello.
Bello dai na ci gaba da kushe allurar rigakafin korona, wadda a yanzu kasashe kusan 50 a duniya ke ta tseren samarwa a kuma mallaka.
“ Wai ana cewa an samo rigakafin cutar korona a cikin shekara daya da bayyanar cutar. Alhali kuma har yau an kasa samun rigakafin cutar kanjamau, zazzabin maleriya, sankara da wasu cututtuka masu yawa da ke kashe mutane.
“Duk mai hankali ya waiwaya baya, ya tuna abinda ya faru a Kano, lokacin da aka gurgunta kananan yara masu yawa, wadanda aka yi wa allurar gwajin rigakafin foliyo.
“Mu dai mun dauki darasi. Ba za a yi mana rigakafin korona ba.”
“Idan sun ce za su yi ta su allurar a gaban idon jama’a, ku rabu da su, can su je su karata. Kada ku ce na ce kada a yi maku rigakafi. Amma duk wanda ya ga zai iya kai kan sa a dankara masa allurar rigakafi, to ya bude idon sa tangaram, kafin ya saida ran sa a yin masa allurar.” Inji Yahaya Bello.
Idan ba a manta ba, Yahaya Bello ya sha karyata cutar korona. Har hanawa ya yi a rika yin gwaji a jihar sa.
Akwai ma lokacin da ya fatattaki jami’an Hukumar NCDC daga jihar, wadanda ya ce idan ya bude ido ya gan su a gaban sa, zai sa a kulle su a killace su tsawon makonni uku. Ya ce ba zai yarda su kai korona jihar Kogi daga Abuja ba.
Bello wanda shi ne gwamna mafi karancin shekaru, ana rade-radin ya na son fitowa takarar shugaban kasa a karkashin APC, kamar yadda kakakin jihar Kogi ya fara yi masa kamfen.