A ranar Talata Gwamnatin Kano ta sanar da samun karin mutum 40 da suka kama cutar korona a jihar.
Gwamnati ta ce ta samu wannan sakamako ne bayan gwajin cutar da aka yi wa mutane 286 a jihar ranar Litini.
Jihar Kano ta samu wannan kari ne a dalilin sake darkakowar cutar korona a kasar nan kuma ta bayyana a shafinta ta tiwita ‘@KNSMOH’.
Gwamnati ta kuma ce an salami mutum 48 da suka warke daga cutar a cikin awa 24.
Tun bayan bayyanar cutar a watan Faburairu mutum 2,364 ne suka kamu da cutar daga cikin mutum 58,765 da aka yi wa gwaji.
Zuwa yanzu cutar ta yi ajalin mutum 68 sannan an sallami mutum 1,978 a jihar.
Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 1,204 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Litini.
Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Litini sun nuna cewa Legas ta samu karin mutum –654, FCT-200, Filato-60, Kaduna-54, Kano-40, Rivers-30, Edo-28, Nasarawa-25, Kebbi-19, Bauchi-18, Oyo-13, Akwa Ibom-12, Bayelsa-11, Ogun-11, Delta-9, Abia-8, Benue-5, Imo-3, Borno-2, Sokoto-1 da Osun-1.
Yanzu mutum 91,351 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 75,699 sun warke, 1,318 sun rasu.Sannan kuma zuwa yanzu mutum 14,267 ke dauke da cutar a Najeriya.