Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 1,861 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Laraba.
Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Laraba sun nuna sun nuna cewa Legas ta samu karin mutum –773, FCT-285, Oyo-138, Rivers-111, Filato-92, Nasarawa-83, Kaduna-59, Enugu-57, Imo-57, Edo-43, Kano-27, Kwara-20, Ebonyi-19, Abia-17, Ogun-12, Osun-12, Katsina-8, Bayelsa-6, Bauchi-5, Delta-5, Borno-4, Jigawa-4 da Zamfara-1.
Yanzu mutum 126,160 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 100,365 sun warke, 1,543 sun rasu. Sannan zuwa yanzu mutum 24,252 ke dauke da cutar a Najeriya.
Ranar Talata , mutum 1,303 suka kamu a Najeriya, jihohin Filato, Edo, Nasarawa, Rivers, Kwara da Babban birnin Tarayya, Abuja ne suka fi yawan wadanda suka kamu.
Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum –46,935, FCT–16,341, Filato –7,740, Kaduna–7,458, Oyo–5,232, Rivers–5,093 Edo–3,646, Ogun–3,251, Kano–2,889, Delta–2,249, Ondo–2,222, Katsina–1,812, Enugu–1,738, Kwara–1,887, Gombe–1,581, Nasarawa–1,720, Ebonyi–1,393, Osun–1,470, Abia–1,220, Bauchi–1,136, Borno-900, Imo–1,046, Sokoto – 707, Benue 749, Akwa Ibom–783, Bayelsa 655, Niger–688, Adamawa–631, Anambra–720, Ekiti–532, Jigawa 450, Taraba 349, Kebbi 267, Yobe-221, Cross River–189, Zamfara 194, Kogi–5.
Shugaban hukumar kula cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko na ƙasa NPHCDA Faisal Shu’aib ya karyata labaran da ake yadawa wai rigakafin Korona karya ce cuta ce ake neman a dirka wa mutanen Najeriya.
Faisal ya bayyana cewa babu wani ciri na makirci da aka yi game da maganin rigakafin Korona kamar yadda wasu ke fadi.
” Maganin rigakafin Korona magani ne da aka hada shi ta hanyar bin dokoki da sharuddan hada magunguna da kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO ta tsara.
” Babu wani guba da aka saka a cikin ruwan maganin da zai illatar da mutane a kasar nan.”
Discussion about this post