KORONA: An ruguje gidajen karuwai saboda kauce wa bin dokar hana cinkoson jama’a

0

Mahukuntan Hukumar Kula da Babban Birnin Tarayya Abuja da kewaye sun bayyana ruguje wani hidan karuwai da aka ce an yi an yi da su rika bin dokar hana cinkoson jama’a saboda korona, amma sun ki bin dokar.

“Mun sha gargadin su ba sau daya ba, kuma ba sau biyu ba cewa su daina abin da su ke yi a ciki, amma sun ki bari. Idan ka zo nan da dare, za ka samu mutum ya kai 5,000, a wurin da bai fi ya dauki mutum 500 ba.”

Shugaban Rundunar Rusau ta FCT, kuma Shugaban Kwamitin Tilasta bin Dokar Korona, Attah Ikharo, ya ce sun rusa gidan karuwan wanda ke Daki Biyu ne saboda ya karya dokar korona.

Ya ce abin da ake tabkawa a gidan barazana ce ga rayuwar jama’a, kuma su na yada cuta a cikin al’umma a daidai wannan laokaci da korona ce kara fantsama.

DAKI BIYU: Amfanin Zunubi Romo:

Dama cikin Satumba sai da jami’an su ka je kauyen Daki Biyu su ka ruguza gidaje akasari duk na karuwai.

Daki Biyu kauye ne mai dauke da dandazon ‘yan kama-wuri-zauna masu rayuwa a wulakantaccen wuri.

Cikin 2016 PREMIUM TIMES ta yi bincike kuma ta buga rahoton yadda karuwai suka yi kaka-gida a Daki Biyu. Sannan kuma mabukata holewa ke karakainar zuwa wurin su ka sheke-aya.

Akwai wasu fitattun gidan holewa a Daki Biyu guda uku, wato Chris Garden, sai kuma Gidan Drama da Gidan Karuwai. Da Gidan Dirama da Gidan Karuwai duk Hausawa ne karuwanda ke ciki.

Wadannan gidajen karuwai duk an ruguza su a cikin Satumba, wurin ya zama fili.

Sai dai kuma makonni kadan bayan ruguza gidajen, masu wurin su ka yi kunnen-uwar-shegu da hukuma, su ka sake tayar da bango, su ka ci gaba da gudanar da harkoki.

Wannan bijire wa doka ce ta kai ga an sake ruguza gidajen biyu a ranar Talata.

Gidan drama da Gidan Karuwai su ka kallon ofishin Hukumar CCB da ke Jabi.

Dama kuma jama’a da daman a kukan yadda ake yin cincirindo a wuraren, musamman a wani Gidan Dambe da shi ma aka ruguza.

Share.

game da Author