Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 1585 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Asabar.
Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Asabar sun nuna cewa Legas ta samu karin mutum –573, FCT-182, Filato-162, Gombe-81, Oyo-75, Rivers-68, Sokoto-58, Ondo-55, Ogun-42, Nasarawa-40, Akwa Ibom-36, Edo-31, Kaduna-27, Anambra-22, Delta-19, Kano-17, Osun-17, Ebonyi-16, Katsina-14
Niger-14, Bayelsa-9, EKiti-8, Borno-7
Jigawa-5, Abia-4, Bauchi-3
Yanzu mutum 99,036 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 79,417 sun warke, 1,350 sun rasu. Sannan zuwa yanzu mutum 18,296 ke dauke da cutar a Najeriya.
A ranar Juma’a, mutum 1,544 suka kamu a Najeriya, jihohin Legas, Filato, Oyo, Nasarawa, Rivers da Babban birnin Tarayya, Abuja ne suka fi yawan wadanda suka kamu.
Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 35,448, FCT –13,406, Oyo – 4,323, Edo –3,060, Delta –1,982, Rivers 3,886, Kano –2,435, Ogun–2,668, Kaduna –5,779, Katsina -1,687, Ondo –1,918, Borno –830, Gombe –1,359, Bauchi –1,082, Ebonyi –1,147, Filato – 5,711, Enugu –1,455, Abia – 1,086, Imo –789, Jigawa –415, Kwara –1,495, Bayelsa –569, Nasarawa – 1,091, Osun –1,063, Sokoto –529, Niger – 477, Akwa Ibom – 512, Benue – 553, Adamawa – 471, Anambra – 364, Kebbi –223, Zamfara –112, Yobe – 201, Ekiti –434, Taraba- 226, Kogi – 5, da Cross Rivers – 169.
Sakamakon gwajin cutar Korona da aka yi a kasar Amurka Kuma aka fitar ranar Alhamis ya nuna cewa akalla mutum 4,000 sun rasu cikin awa 24 a kasar.
Wannan shine karo na farko da kasar ta samu yawan mutanen da suka rasu a rana daya a wannan lokaci.
Bisa ga rahotan jaridar ‘Washington Post mutum 3900 ne suka mutu a dalilin kamuwa da cutar a kasar ranar Laraba.
Masana kimiya da masana magungunan sun hada maganin rigakafin korona kuma kasar Amurka na daga cikin kasashen da suka fara amfani da su sai dai duk da haka mutane sai kara mutuwa suke a dalilin cutar.
Sakamakon jami’ar John Hopkins ya nuna cewa mutum miliyan 21.5 ne suka kamu da cutar a kasar zuwa yanzu. Daga ciki mutum 364,500 sun mutu.
Discussion about this post