Wa’adin ficewa daga dazukan Jihar Ondo cikin kwanaki bakwai da Gwamna Rotimi Akeredolu ya bai wa Fulani makiyaya, ya fara tayar a kura tsakanin Kungiyar Dattawa Yarabawa Zalla (YCE) da kuma Kungiyar Dattawan Arewa (NEF)
Yayin da Kungiyar Dattawa Yarabawa Zalla ke goyon bayan Gwamna Akeredolu, su kuma Kungiyar Dattawan Arewa sun yi kira ga duk wani Bafulatani makiyayi da ke cikin dazukan jihar Ondo, ya yi zaman lafiya da jama’a. amma kuma kada ya sake ya tashi.
Kungiyar ta Dattawan Arewa ta ce duk wani makiyayin da ke zaune lafiya da jama’a ya yi zaman sa, kada wata barazana ta tayar masa da hankalin har ya yi tunanin tashi.
Tuni Ya Kamata A Kori Fulani Makiyaya – Dattawan Yarabawa
Ita dai Kungiyar Dattawa Yarabawa Zalla (Yoruba Elders Forum), ta ce ai tuni ne ma ya kamata a ce an fatattaki Fulani makiyaya daga cikin dazukan-gwamnatin jihar Ondo din.
Cikin wani jawabi da YEF ta fitar bisa sa hannun Babban Sakataren YEF, Kunle Olajide, ya ce tuni ya kamata a ce an fatattaki makiyayan, “saboda ai babu wata doka a Najeriya da ta ce wani daga wata jihar na da dama shiga wata jiha ya mamaye masu kasa, ya rika lalata masu amfanin gona ya na tayar da fitina, kuma jama’ar yanki su yi tsaye su na kallon sa.
“Dajin nan Dajin-gwamnati ne, amma kuma tun cikin 2015 makiyaya sun mamaye shi, su na lalata mana amfanin gona, su na kashe mana mutanen mu. Su na yi wa mata fyade. Kuma su na yin garkuwa da mutane, ana kai masu kudin fansa.
“Amma kuma abin takaici gwamnatin tarayya da jami’an tsaro sun kauda kai, sun toshe kunnuwan su daga kukan da mu ke yi masu.”
Dattawan sun nuna goyon gaya 100 bisa 100 ga Gwamna Akeredolu na korar makiyaya.
Kada Wani Makiyayin Da Ya Fice Daga Jihar Ondo –Dattawan Arewa
Sai dai kuma kakakin yada labarai na Kungiyar Dattawan Arewa, Hakeem Baba-Ahmed, ya yi kira ga Fulani Makiyaya da ke zaune Jihar Ondo cewa kowa ya yi zaman sa lafiya. Amma kada wanda ya fice daga jihar. “Kungiyar Dattawan Arewa na cike da mamakin rahoton da aka watsa cewa Gwamna Rotimi Akeredolu ya bai wa makiyaya wa’adin ficewa daga jihar Ondo. Yaya mutumin da ya kai matakin SAN a shari’a zai yi wannan kasassabar, ya kori mutanen da ke zaune wata jiha tsawon shekara da shekaru.” Inji Dattawan Arewa.
“Ai babu wani dan Najeriya da ke da ikon korar wani dan Najeriya daga wani wurin da ya ke zaune. Don haka kungiyar mu na ganin matakin da gwamnan ya dauka, zai iya tunzira jama’a kuma ba zai haifi da mai idanu biyu ba.”
“Idan akwai masu laifi accikin Fulanin, to alhakin gwamna ne ya dauki matakin duk da ya dace a zakulo su a hukunta su. Kuma babu inda Fulani ke da wata dokar kariyar kin fuskantar sharia’a idan sun yi laifi a Najeriya.”
PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda Akeredolu ya maida wa Fadar Buhari martani cewa ta fi tausayin Fulani makiyaya fiye da sauran ’yan Najeriya –Jihar Ondo
Gwamnatin Jihar Ondo ta maida wa Fadar Shugaba Muhammadu Buhari raddi, dangane da yadda fadar ta yi kakkausan suka ga jihar Ondo, don ta bada wa’adin kwanaki bakwai ga Fulani makiyaya da ke cikin dazukan-gwamnatin jihar cewa su fice daga ciki.
Kamishinan Yada Labarai na Jihar Ondo, Donald Ojogo, ya bayyana cewa martanin da Kakakin Fadar Shugaban Kasa, Garba Shehu ya yi a Ondo, ya fi kama da cea fadar ta fi nuna tausayi ga Fulani makiyaya fiye da ko a kasar nan.
“Furucin Garba Shehu ya nuna inda fadar gamnatin tarayya ta fi nuna tausayi. Hakan dai babbar barazana ce ga dorewar zamantakewar jama’ar kasar nan a wuri daya.” Inji Ogoja.
“Mu na neman karin bayani daga gamnatin tarayya a yi mana dalla-dalla shin ko rashin mutuncin da masu fakewa da kiwo ke yi su na garkuwa da mutane, ko sun dogara ne da jingina ga bangon masu mulkin da su ke takama ne? Gaskiya ana yi a hakin kankasar nan barazana.”
Tankiyar ta samo asali tun daga ranar Litinin, bayan Gwamna Rotimi Akeredolu ya haramta wa makiyaya kiwo a cikin dajin-gwamnatin jihar Ondo.
A martanin Fadar Shugaban Kasa, Garba Shehu ya bai kamata a tauye wa makiyayan hakkin su na kiwo ba. Kamata ya yi a zauna a sasanta, a fitar da baragurbi daga cikin su.
Gwamnatin Jihar Ondo ta maida martani kamar haka:
“Abin tambaya a nan, shin wai wadannan makiyaya masu kashe mutane su na garkuwa su na fashi da makami, sun fi sauran jama’a da ita kan ta Gwamnatin Tarayya muhimmanci ne?
“Kuskure ne mutum ya fake cikin fadar shugaban kasa ya na fitar da maitar sa ta kabilanci a fili.”
PREMIUM TIMES ta tuntubi Ogoja a ranar Laraba inda ya tabbatar mata cewa ya yi wannan bayani.
Sannan kuma ya ce wa’adin da aka ba makiyayan na nan, ba za a fasa fatattakar su ba.
PREMIUM TIMES HAUSA ta bada labarin yadda Gwamnatin Ondo ta fatattaki Fulani makiyaya daga dazukan Jihar, tare da tukuicin tsauraran dokoki shida.
Gwamnan Jihar Ondo Rotimi Akeredolu, ya umarci dukkan wasu Fulani makiyaya da ke zaune cikin dazukan jihar (forest reserves), su fice daga cikin dajin nan da kwanaki bakwai.
Umarnin ko kuma dokar ya fara aiki ne daga ranar Litinin 18 Ga Janairu, 2021.
Akeredolu ya bada wannan umarnin ne a lokacin da ya yi ganawa tare da shugabannin Fulani makiyaya da kuma shugabannin kabilar Ebira da ke jihar.
Taron ya gudana a Babban Dakin Taro na Cocoa Conference Hall da ke cikin Gidan Gwamnatin Jihar Ondo a Akure, babban birnin jihar.
Akeredolu ya ce an dade ana fama da hare-hare da garkuwa da mutane wadanda wasu batagari ke yi da fakewa da kiwo amma su na garkuwa da mutane a jihar.
“A yau mun dauki babban matakin farko na dakile garkuwa da mutane da saukar manyan laifukan da ake aikatawa a fadin jihar nan.”
“Yawancin wadannan ayyukan garkuwa da mutane wasu batagari ne ke yin su masu fakewa da sunan makiyaya. Sun maida dazukan gwamnati wata mabuyar masu garkuwa da mutane, su na karbar makudan kudaden diyya.
“A matsayi na na Gwamnan Jiha wanda nauyin kare hakkin rayuka da dukiyoyin jama’a ke hannun sa, ina sanar da bijiro da wadannan ka’idojin da gaggawa, wadanda su ka hada da:
Tsauraran Dokoki 6 Da Gwamnatin Ondo Ta Kakaba Wa Makiyaya:
1. Makiyaya su gaggauta ficewa daga dukkan dazukan gwamnati da ke cikin jihar Ondo, nan da kwanaki bakwai, daga ranar Litinin 18 Ga Janairu, 2021 za su fara kirgawa.
2. An haramta kiwo cikin dare, saboda yawancin gonakin da makiyaya ke cinye wa amfanin gona, duk da dare ake yin aika-aikar.
3. An haramta zirga-zirgar shanun kiwo a kan manyan titina da kuma cikin gari.
4. An haramta kiwo ga duk wani yaron da ba balagi ba.
5. An umarci dukkan jami’an tsaron da ke Jihar Ondo su tirsasa bin wannan dokar tilas.
6. Amma gwamnatin mu mai tausayi ce, don haka duk wani mai son yin kiwo a jihar nan, to ya gaggauta yin rajista da hukumar da nauyin kula a kiwo ke kan ta.