KOFIN FA: Liverpool ta lallasa Aston Villa da ci 4-1

0

Kungiyar Kwallon kafa ta Liverpool la lallasa Aston Villa da ci 4 -1 a gasar cin kofin FA da ake bugawa a kasar Ingila.

Dan wasan Liverpool, Sadio Mane ne ya fara jefa Kwallo a ragar Aston Villa tun a farkon rabin lokaci. Kafin a tafi hutun rabin lokaci, Aston Villa ta barke kwallon ta hannun Loui Barry.

Bayan an dawo hutun rabin lokaci sai Liverpool suka fara yi wa Aston villa luguden kwallaye a ragar su.

Georginio Wijnaldum ya jefa kwallo ta biyu a daidai minti 60 da wasa, Shaqiri, Mani da Salah suka karkare sauran kwallayen.

A wasa na biyu da aka buga, Wolves sun doke Crystal Palace da ci daya mai ban haushi.

Adama traore ne ya jefa kwallon tun a farkon rabin lokaci.

Share.

game da Author