Ko zazzaɓi ke damun ka, kallon mai cutar korona za mu yi maka –Gwamnan Legas

0

Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanyo-Olu ya bayyana cewa daga yanzu ko alamun zazzaɓi ke damun mutum, to za su dauka cewa cutar korona ce ke damun sa. Sai fa idan an auna an tabbatar ba ita ba ce.

Wannan bayani na sa ya biyo bayan ganin yadda ake ta samun yawan fantsamar cutar korona a Jihar Legas.

Haka dai gwamnan ya furta a ranar Talata.

Daga nan sai ya shawarci duk ma wani mai jin wata ko wasu alamomin zazzaɓi ko masassara ya garzaya cibiyar gwajin cutar korona domin a auna shi ba tare da ya biya ko sisi ba.

Ya yi tsokacin cewa akwai muhimmanci sosai mutum ya garzaya tun da wuri a auna shi, ta yadda idan har korona ce ke damun sa, to za a iya tarar ciwon da wuri, tun kafin ya kwantar da mutum ko kuma kashe shi dungurugum.

Da ya ke jawabi a taron manema labarai Lagos House da ke Ikeja, Sanwo-Olu ya ce akwai bukatar mazauna Legas su shiga taitayin su da wannan cuta. Yin haka inji shi zai taimaka wa kokarin da gwamnatin jihar ke yi wajen dakile cutar a daidai wannan lokacin da ta ke kara fantsama bagatatan.

Ya ce irin yadda korona ta sake darkakar Lagos a karo na biyu ya sa tilas bukatar tukunyar iskar da ake shaka a cibiyoyin kula da masu korona ya karu sosai.

Dalilin sake fantsamar korona ce ta sa aka sake bude wasu cibiyoyin kula da masu cutar, wadanda a baya aka kulle.

“Cikin makonni kadan baya da su ka gabata, bukatar tukunyar bututun iskar da marasa lafiya ke shaka ya karu daga tukunya 70 a rana daya zuwa tukunya 350 a rana daya, kuma kowace tukunya mai cin lita shida ta iskar da ake shaka a Babban Asibitin Mainland da ke Yaba, Lagos.” Inji Gwamna.

Share.

game da Author