Ko kotu ta rabani da matata ko ayi mace-mace a gida na – Magidanci

0

Wani malamin makaranta mai suna Yemi Ogayemi ya shigar da kara a kotun dake Jikwoyi a Abuja yna rokonta ta raba aurensa kafin matarsa Fumi ta kashe shi ko ta kashe kanta.

Yemi mazaunin Jikwoyi ya ce ba zai iya zama da matar da daga sun dan samu sabani sai ta nemi kashe shi ko kanta ba.

Ya ce Fumi ta yi alkawarin cewa idan har dai bata kashe shi ba za ta kashe kanta ta hanyar da dole shine za a ce ya aikata kisan.

” Wata rana da sabani ya shiga tsakanin mu sa kawai ta waruri sharbeben wuka ta danno kai na, badun Allah ya sa na yi gaggawar fallawa da gudu ba da yanzu ina barzahu.

” Sannan kuma akwai randa ta wawuri almakashi ta kekketa kayan sawa na da takalma na masu tsada saboda na bata naira 3000 ta je kitso bayan ita kuma naira 7000 take bukata tayi irin wannan kitso. Ni kuma a lokacin bani da naira 7,000 din da zan iya bata domin ta yi kitso da shi.

A nata jawabin a gaban alkali, Fumi ta yarda da duk laifukan da mijin ta ya ce ta aikata sai dai ta ce ta yi ta neman gafaran sa tun lokacin, hasali ma ta ce duk ranar da suka samu sabani irin haka sai ta nemi gafarar sa.

“A gaskiya ban ji dadin ganin mu a kotu ba, bayan ko na roke shi yayi hakuri kuma yakan ce ya yafe min.

Alkalin kotun Jamilu Jega ya dage shari’ar zuwa ranar 9 ga Maris 2021.

Share.

game da Author