Ko gwamnati ta fadada aikin wayar wa mutane kai game ‘Rigakafin Korona’ ko ta kwan ciki – Bafarawa

0

Tsohon gwamnan Jihar Sokoto ya yi kira da a karfafa kamfe din fadakarwa, musamman a yankunan karkara, gabanin isowar alluran rigakafin Korona a kasar.

Tsohon gwamnan, ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai a ranar Laraba a Abuja, yayin da yake magana kan barkewar Korona a karo na biyu da sauran batutuwan kasa.

Bafarawa ya ce ya kamata gwamnati ta sanya karin matakai don dakile yaduwar kwayar cutar a kasar nan.

Ya kara jaddada cewa kara karfafa kamfen da wayar da kan jama’a na da matukar muhimmanci kasancewar mafi yawan ‘yan Najeriya ba su yarda cewa akwai kwayar cutar ba.

“ Dole gwamnati ta maida hankali wajen karfafa yin kamfen da wayar wa mutane kai mutane tun da wuri gudun kada a samu matsala a lokacin da za a fara yi wa mutane rigakafin maganin Korona. Idan ba a yi haka ba kuwa to za a iya tafka asara domin da yawa ba za su yi ba.

“Akwai mutane da dama da ke karkara wanda har yanzu basu san wannan cuta ba, wasu kuma da dama basu yarda akwai ta ba. Dole a fadada kamfen din wayar wa mutane kai daga birane har zuwa can cikin karkara su yarda kuma su amince da shi.

Wadannan, in ji shi, suna daga cikin batutuwan da ya kamata Gwamnatin Tarayya ta kara mai da hankali a kansu, don ganin aikin ya zama mai amfani kuma an samu nasara.

Dangane da kalubalen tsaro da kasar ke fuskanta, Bafarawa ya ce akwai bukatar a dwao a hada hannu wuri daya yana cewa hakkin kowa ne tabbatar da tsaro a kasa.

“Kowane ɗayanmu a matsayinmu na membobin al’umma ya kamata mu tuna cewa yayin da gwamnati ke yin abin da ya kamata ta yi muma mu rika yin namu kokarin.

Share.

game da Author